wasa tsakanin real Madrid da man city Yaya hasashen ka ??

Yau Juma'a za'a cigaba da buga gasar cin kofin nahiyar zakarun Turai wato (UEFA champions league) da aka dakatar tun watan February a sakamakon ɓullowar cutar coronavirus. Wasa mafi ɗaukar hankali da za'a buga a yau shine, Real madrid da Manchester city wanda za'a buga a gidan Mancity wato wasan Zagaye na biyu. Wasan farko Mancity ta doke Real madrid daci 2_1 a filin wasa na Santiago wanda hakan ne yasa wasu ke kallon an riga an kori Real madrid daga gasar. HAR YANZU AKWAI SAURAN RINA A KABA. A matsayina na mai goyon bayan Real madrid Banso nace komai ba dangane da wannan wasa, a sakamakon wasu dalilai, sai dai ni dama can banji a jikina cewar za'a kori Real madrid ba, sabida ba baƙon abu bane a doke Real madrid a gidanta daga bisani taje gidan ƙungiya ta doke ta har gidanta kuma komai girman ta, wannan ba baƙon abu bane a Tarihin Real madrid. A shekarar 1988 Bayern Munich ta doke Real madrid a gidanta daci 2-3 amma Real madrid ta bita har gida ta doke ta daci 2 _ 0, sannan a shekarar 1990 Ajax ta doke madrid daci 1 _ 0 a gida, daga bisani Real madrid ta bita har gida ta doke ta daci 2 _ 0. Sannan 1988 Bayern Munich taci madrid 4 - 2 a gida, daga bisani Real madrid ta bita har gida ta doke ta daci 4 - 1. Irin wannan yanayi yasha faruwa, kuma Real Madrid babu wani filin wasa da batayin nasara a Tarihin gasar cin kofin nahiyar zakarun Turai, kuma itace ƙungiyar da tafi kowacce yawan samun nasara a waje, don haka abune mai sauki Real madrid tayi waje da Mancity a wannan wasa. ABUBUWAN LURA AKAN WANNAN WASA. 1. Real Madrid da Mancity suna cikin yanayi mai kyau, saidai Real madrid tafi ƙorari a wasannin da suka gaba bayan dawowa daga hutun coronavirus. A cikin wasanni 10 da ƙungiyoyin suka buga Real madrid ta lashe wasanni 9 acikin 10, sannan sai kunnen doki guda 1 WWWWWWWWWD. Ita kuwa Mancity taci wasanni 8 a cikin 10 sannan tayi rashin nasara sau 2 bayan dawowa hutun coronavirus WWWWWWLWLW. 2. Real madrid ta doka wasanni guda 5 a gida kuma ta lashe gaba ɗaya, sannan itama Manchester city ta buda wasanni guda 5 a gida itama ta lashe gaba ɗaya. Tun da aka dawo hutun Coronavirus Real madrid bata taɓa yin rashin nasara a waje ba, haka ita kuma Manchester city bata taɓa yin rashin nasara a gida ba saidai a waje. Don haka akwai damar da Real madrid zata iya kare wannan nasara, haka itama Manchester city zata iya kare wannan nasara duba da suma suna da kyau sannan zasu buga wasa ne a gida. 3. A haduwar farko da Madrid tayida man City, lokacin Real Madrid batakan ganiyarta awasan alokacin wadda hakan yataka mahimmiyar rawa wajen taimakon man city hartayi nasara akan real madrid. Amma wani abu shine, awasau lokutan Madrid nashan wahala a wasannin gida musamman awasan champion league kamar yadda mukabi diddikin yadda wasu wasanni nata suka gabata ashekarun baya. 4. A wasan farko Real madrid tayi wasane batare da eden hazard da ake kallon jigo ne a wasan kasancewa ya saba haɗuwa da ƙungiyar domin jinyar dayake famada ita alokacin. Yanzu ya sami cikakkiyar lafiya da zai tunkari karawar. 5. A halin yanzu Manchester city suna da matsalar ƴan wasa baya wato 5 & 6 wanda shi kansa Guardiola ya koka da matsalar jinya da ƙungiyar ke fama ita na rashin wasu ƴan wasa a halin yanzu Sergio Aguero yana Jinya, sannan Benjamin Mendy an dakatar dashi daga buga wasan kamar yadda aka dakatar da Sergio Ramos. Yanzu haka babar matsalar Real madrid shine, rashin takamaiman ɗan wasa da za'a kalla asa rai koda yaushe zai jefa kwallo a lokacin da ake buƙata shi yasa a bana Real madrid tafi cin wasa da ƙwallaye 2, ko 1, saidai duk da haka tana ƙoƙari don ganin cewa Ƙwallaye basu shiga ragar ta ba. Wannan wasa yana da matuƙar hatsari, kuma yana da muhimmanci a gareta, kuma zasuyi iya iyawarsu domin lashe wannan wasa koda daci 3 _ 2 ne. Saidai ita ƙwallon kafa ba haka take ba, tana iya zuwa da sakamakon da ba'a zata ba, amma ina jin ƙarfin guiwar cewar zasuyi nasara. 07/08/2020

Post a Comment

0 Comments