shin tsakanin messi da pele wanene yafi bajinta A ƙwallon ƙafa?








Bayan Muhawarar data guda a jiya ta yan wasan da suka taɓa sanya riga mai lamba 10 ne na buƙaci jin ra'ayoyin al'umma akan wanne Ɗan wasa ne yafi taka rawar gani a cikin su. Saidai Messi Da Pele sune waɗanda sukafi ɗaukar hankali a Tarihi, inda wasu suka buƙaci a ɗanyi tsokaci akan rawar da kowane ya taka a kwallon kafa.

A Tarihin ƙwallon ƙafa Har yanzu yan wasan ƙwallon kafa, da masana ƙwallon kafa, da masu kallon ƙwallon ƙafa na kallon Pele a matsayin abu a kwallon kafa wanda ba'a taɓa yin kamarsa ba a Tarihin ƙwallon na duniya baki ɗaya, duba da shine ɗan wasan da yafi kowanne Lashe kofin duniya wato (world cup) inda ya lashe kofin har sau 3, kuma ya fara lashe kofin tun Yanada shekara 17. Dalili na gaba kuma shine, Anata yaɗa wani labari dake bayyana cewa Pele ya jefa kwallaye 1,281 a cikin wasanni 1,363 daya buga a kakar wasanni 19 na tsawon zamaninsa a fagen ƙwallon ƙafa.

Shin Yaya A abun yake?

-PELE

To Da farko dai bari na ɗan yi waiwaye akan Rawar daya taka a fagen wasanni.
Bincike ya nuna cewa batun da akeyi na cewa Pele ya jefa kwallaye 1,281 a cikin wasanni 1,363 daya buga wannan gaskiya ne, saidai bincike ya tabbatar da cewa gabaki ɗaya kwallayen daya jefa a raga aka lissafa, cikinsu harda wasannin sada zumunci, da dukkan wani wasa daya taɓa bugawa wato (Official and Unofficial goals). Amma daga bisani da aka tantance adadin sahihan kwallaye daya jefa (Official goals) Pele ya jefa kwallaye 650 a raga a cikin wasanni 694 a ƙungiyoyin Santos da New York Cosmos a  ƙasar Brazil kuma ya buga wasanni 92, sannan ya jefa kwallaye 77. Idan ka haɗa wasannin daya buga a kungiyoyi da ƙasar sa da kwallayen daya ya jefa, gabaki ɗaya ya buga wasanni 786, sannan ya jefa kwallaye 727.
Gabaki ɗaya Pele ya lashe kofuna 30, guda 25 a Santos, Guda 2 a New York Cosmos, guda 3 a Brazil Wato World cup.

Lambobin Yabo.

Pele ya lashe lambobin yabo guda 70, daga cikin su akwai :

-A shekarar 2000 ne aka basa kyautar Gwarzon ɗan wasan da babu kamarsa a wannan ƙarni wato (FIFA Player of the Century)
-A shekarar 2013 ne aka Bawa Pele Kyautar Ballon D'or (  FIFA Ballon d'Or Prix d'Honneur : 2013) ta yabo a sakamakon ya chanchanci lashe kyautar tun yana wasa amma bai lashe ba sakamakon bai taɓa buga wasa a ƙungiyar Turai ba, haka bai taɓa buga gasar cin kofin nahiyar zakarun Turai ba wanda shine abu da akafi la'akari dashi wajen lashe kyautar.
-Sannan ya lashe kyautar France Football 's Ballon D'or sau  7: 1958, 1959, 1960, 1961, 1963, 1964, 1970 .

Har ila yau Pele yana da waɗansu ragowar Tarihi guda  20 da ba' a karya ba, kuma babu wani ɗan wasa dayake dasu ko ya taɓa kafa su a Tarihin ƙwallon. Waɗannan Tarihi sun haɗa da:

-Ɗan Wasa mafi ƙarancin shekaru daya fara buga gasar cin kofin duniya yana da shekaru 17 da kwana 239, sannan shine mafi ƙarancin shekaru daya jefa kwallo a gasar, sannan shine mafi ƙarancin shekaru daya jefa kwallaye uku a wasa ɗaya, sannan shine mafi ƙarancin shekaru daya lashe world cup.
-Shine Ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru daya lashe kofin sau 2 a jere yana da shekaru 21. Etc. Yanzu haka Pele ne ɗan wasan da ake ganin ƙimarsa kuma ake masan kallon wanda babu kamarsa a koda yaushe.

LIONEL Messi.

Shima yana Daga cikin yan wasan ƙwallon kafa da sukafi fice a waɗanda suka goya riga mai lamba 10, kuma yana daga cikin yan wasan ƙwallon kafa na duniya da babu kamar su. Lionel Messi Shine ɗan wasan da babu kamarsa a gasar Laliga da kuma ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barcelona.
A gabaki ɗaya Messi ya jefa kwallaye 697 a ƙungiyar Barcelona da kuma ƙasar Argentina a tsawon shekaru 19 da yayi yana buga wasa wato daga 2001 zuwa 2020.

Ya lashe kofuna guda 33, waɗanda suka hada da Champions League, Laliga.
Ya lashe lambobin yabo guda 104 da suka haɗa da Ballon D'or guda 6, Gwarzon Dan wasan laliga guda 6, Golden boy award guda 1,World Soccer Player of the Year Guda 5 da sauran su.

Bambanci tsakanin Pele da Messi.

-Pele Ya gama bajintarsa ta ƙwallon ƙafa a yankin Latin.
-Messi kuwa yana ƙwallon kafa a Turai.
-Pele: ya lashe ma ƙasar sa ta Brazil manyan kofuna da suka haɗa da kofin duniya guda 3.
-Messi: Tun lokacin daya shahara bai taɓa lashe ma ƙasar sa wani babban kofi ba, sai ya lashe FIFA U-20 World Cup, 2005, sai  Argentina U23 Summer Olympics: 2008.
-Pele Yana da kyautar France Football 's Ballon D'or sau  7: 1958, 1959, 1960, 1961, 1963, 1964, 1970. Da kuma Ballon D'or Prize 2013.
-Messi: Ya lashe FIFA Ballon D'or sau 6, Sai kyautar Gwarzon Dan wasan nahiyar Turai sau 3.
-Pele: ya buga wasanni 786, sannan ya jefa kwallaye 727.
-Messi: Ya buga wasanni 627, ya jefa kwallaye 697.
-Pele ya lashe kofuna 39 Da suka haɗa da world cup guda 3.
-Messi ya lashe kofuna guda 33 da suka haɗa Champions League guda 4.
-Pele: ya lashe lambobin yabo guda 70.
-Messi ya lashe lambobin yabo guda 104.
Idan mukayi duba zamuga Pele yafi Messi buga wasanni, sannan ya fisa cin kwallaye, sannan ya fisa lashe kofuna. Shi kuwa Messi lambobin yabo yafi Pele lashe wa, saidai mafi akasarin lambobin yabon da Pele ya lashe Messi bai lashe ba, haka shima Messi lambobin daya lashe shima Pele bai lashe ba, sabida bambanci na ƙungiya, Nahiyar da kowanne yayi kwallo, da kuma bambanci na lokaci.

Babu Shakka Pele Shine Ɗan wasan da babu kamarsa a jerin ƴan wasa da suka sanya riga mai lamba 10 dama duniya baki ɗaya a Tarihin ƙwallon ƙafa, sabida waɗannan bajinta da yayi.
Masana sunyi la'akari dasu, sannan ɗan wasane da har ya gama bashi da burin komai daya wuce ya samarwa ƙungiyarsa nasara bawai ya tara kudi ba, tun a 1959 manyan ƙungiyoyi irin Real madrid, Barcelona ke nemansa amma yaki amincewa sabida kishin ƙungiyarsa, kuma Pele bai taɓa barazanar zai bar ƙungiyarsa ba akan kuɗi kamar yadda yan ƙwallon ƙafa keyi a halin yanzu.

Post a Comment

0 Comments