Tuni magoya bayan ƙungiyar ƙwallon kafa ta Real madrid ke turo min da saƙo cewar "Shin Eden Hazard musulmi ne ko kirista?" inda suka buƙaci a basu Tarihinsa domin su san ko wanene shi.
wanene Hazard?
Cikakken sunansa shine Eden Michael Hazard, an haife sa a ranar 7 ga watan January a shekarar 1991 a yankin La Louvière , dake kasar Belgium.
Louvière Wani yanki ne dake da manyan cibiyoyin addinin kiristanci da gidajen Tarihi da suka shahara a nahiyar Turai. Saidai Hazard ba a wannan gari ya taso ba, ya taso ne a wani gari mai suna Braine-le-Comte wanda yawan mutanen yankin yakai kimanin mutane miliyan 3,633,795 a kidayar da aka gudanar a shekarar 2019. Kaso 99% acikin dari na al'ummar wannan gari suna bautar wani addini mai suna Wallonia.
Sunan Mahaifinsa Thierry Hazard, sannan Mahaifiyarsa itace Carine Thierry. Dukkaninsu yan kwallon kafa ne, saidai Mahaifiyarsa ta ajiye ƙwallon kafa ne bayan ta sami cikinsa da wata 3. Sannan Mahaifinsa ya ajiye ƙwallon kafa ne domin ya sami damar kasancewa tare da iyalan sa. Hazard su huɗu ne a wajen iyayensa kuma dukkan su yan wasan ƙwallon kafa ne, a cikin su akwai Thorgan Hazard tsohon dan wasan Chelsea kuma ɗan wasan Brussia Dortmund a halin yanzu.
Shin Menene Addinin Hazard?
Wannan Itace Tambayar da tuni aketa cece-kuce akanta bama a iya nan ba har su kansu a Kasashen duniya a shafukan sada zumunta a sakamakon waɗansu dalilai kamar haka:
-Na farko kawo yanzu Hazard bai taɓa bayyanawa duniya addininsa ba, walau a gidan talabijin etc.
-Na biyu yana nuna ƙauna da kusanci ga addinin guda biyu.
-Hazard bashi da wata tsayayyar alƙibilah da za'a kalla a gane addininsa kai tsaye.
To yaya abun yake?
A zahirin gaskiya Har yanzu ba'a daina tantama akan Hazard musulmi ne ko kirista ba saidai mafi akasarin mutane sun tafi akan cewa Musulmi ne, sannan shafuka da dama sun tafi akan haka.
Hazard ya nuna waɗansu alamu masu rikitarwa akan addinan guda biyu.
Na farko shine, a ranar 1 ga watan Disamba shekarar 2016 EDEN HAZARD yayi wani Rubutu a shafin sa na twetter kamar haka "Christmas starts right here, with my family. I love Christmas is coming" Sannan ya saka hotonsa daya ɗauka acikin taron jama'a, wannan yanayin hoton ɗaukar dare ne, hakan na nuni da cewa, kodai kirista ne ko kuma Yanada alaƙa da kiristanci, ko kuma bashi da tsayayyen addini, wannan shine abinda wasu suka duba suke kiran sa da kirista.
-Na biyu a ranar 20 ga watan jully shekarar 2012 alokacin da watan azumi ya kama Hazard yayi wani Rubutu a shafin sa na Twitter inda yake bayyana farin cikinsa na shigowar wannan wata " Bon Ramadan a tous" ma'ana "Happy ramadan to all Muslims" sannan a kakar wasanni ta 2015-16 an nuno Hazard ya kalli gabas yayi sujjada bayan ya jefa kwallo. Ba'a jima ba sai gashi a fitar da sunayen yan wasa guda 54 a gasar firimiya da suke musulmai kuma sunan Hazard ya shiga ciki a sakamakon waɗancan dalilai. Saidai kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da take bayyana cewa Hazard musulmi ne duba da waɗannan dalilai.
A ina gizo ke saƙar?
-Na farko ba'a taɓa nuna Hazard a wani waje na ibada ba wato Coci ko masallaci ko aikin hajji etc.
-Na biyu ba'a taɓa ji ko ganin ƙungiyarsa ta basa hutu domin yaje aikin hajji ko hutu a sakamakon azumi ba, wanda a bisa al'ada koda Ace gasa ba suje hutu ba to ana rangwantama musulmi.
-Na uku bai taɓa bayyanawa duniya ga takamaiman addinin da yake ba.
-Na huɗu babu wani shafi daya bayyana gaskiyar addininsa da kuma dalilin su na faɗin hakan.
-Na biyar Masu hikima sunce "Suna linzami, babu shakka sunayen Hazard guda biyun farko wato" Eden" da kuma "Michael" sunaye na kiristanci.
Kalmar "Eden" tana da salsala da dama a ciki littafin Genesis Bible dayake bayani akan farkon halittar duniya da kuma samuwar addinin kiristanci, wato littafi na farko da mutanen Hebrew suka wallafa. Kalmar na nufin (Matuƙar jindadi) kai hasalima a kiristancinma sunane daya keɓanta ga mata.
Sannan sai suna na biyu wato Michael wanda shima sunane na kiristanci. A kiristanci idan akace Michael to tamkar irin salon magana ne da take zuwa da tambaya da baya buƙatar amsa wato (Rhetorical Question) misali Ace "Duk cikar mazan garin nan wanene yafi mahaifinka? Kaga ana amsar itace babu. A Addinin kiristanci kalmar Michael na nufin" who is like God? Wato (Wanene kamar Ubangiji ?) Kunga anan mu a muslinci amsar itace babu.
Haka idan muka ɗauki laƙabinsa wato "Hazard" tana nufin abinda yake da matukar hatsari kuma yake haifar da asarar Rayuka da dukiya. Kunga idan muka yi la'akari da wannan suna da waɗannan hujjoji dana bayyana to kai tsaye ba zamu iya kiran Hazard da musulmi ba, sannan ba zamu iya kiransa da kirista ko marar addini ba. Komai dai zai iya faruwa, Kawai Allah ne kaɗai yasan haƙiƙanin addinin dayake bi ahalin yanzu.
0 Comments