wacce moriya Madrid taci da Kareem benzeema ?

Fiye da shekaru 11 Benzema ya kwashe yana buga ƙwallo a Real madrid .
Tun farkon zuwan sa Real madrid babu wanda yayi tsammanin cewar Real madrid zata iya riƙe ɗan wasan harna tsawon waɗannan shekaru, wanda a iya cewa ba kasafai Real madrid ke bawa ƴan wasa irin wannan damar ba dukda ƙarancin jefa ƙwallaye da ɗan wasan yake dashi tun daga shekarar 2009 zuwa 2018, wanda tun wajen shekarar 2012 Real madrid keta neman ɗan wasan gaba wanda yake jefa kwallaye a raga sosai, daga wancan lokacin tayi zawarcin ƴan wasan gaba a ƙalla guda 10 kamar su Diego forlan, Aguero, Falcao, Emmanuel Adebayor, Diego Costa, Luis Suarez, Lewandowski, J. Matinez, L Herry Kane, L. Martinez, Icardi, da sauran manyan ƴan wasan gaba na duniya tun daga wancan lokaci zuwa yau, saidai babu wanda ta ɗauka sai waɗanda suke zuwa a matsayin ƴan chanji.
Bayyanar Zidane a matsayin mai horarwa a Real madrid shine tabbatuwar cigaba da zaman Benzema a Real madrid a sakamakon shine ɗan wasa na farko da zidane ya bayyana zaiyi amfani dasu.
Rabonda Real madrid ta riƙe ɗan wasan gaba wanda ya gota shekara 11 tun lokacin Santillana daga shekarar 1971 zuwa 1988 wanda ya shafe shekaru 17 a ƙungiyar yau shekaru 32 kenan.
A season dinsa na uku wato 2011/2012 Benzema , ya rasa kusan tsawon kakar a sakamakon rauni da yayi, amma bayan da ya dawo ya ci gaba da ƙoƙari a wancan lokacin saidai akan ajiyesa ayi amfani da gonzalo Huiguin.
Tun a lokacin ne Jose Mourinho ya yi tunanin Real madrid ta siyasa masa Emmanuel Adebayor amma saidai haka bai samu ba.
Har yau a ƴan kwanakin nan Real Madrid tayi zawarcin dan wasan gaban Dortmund wato Erling Haaland, amma sun san saboda sanin cewa a duk lokacin data sami wani ɗan wasa to Benzema zai samu saukin buga wasa wanda a yanzu shine jigo a Real madrid.
Tunda zuwan Benzema Real madrid ta samu sauƙi wajen kashe kuɗaɗe domin ɗaukar ɗan wasan gaba ba kamar sauran manyan ƙungiyoyin ƙwallon kafa na duniya ba, misali.
- Barcelona daga 2009 zuwa yanzu ta kashe manyan kudade wajen ɗauko ƴan wasan gaba irinsu Villa, Ibrahimovic da Luis Suarez, Braithwaite yanzu haka suna neman Martinez ido rufe.
- Atletico Madrid, daga wancan lokacin tayi ƴan wasan gaba irinsu: Diego Forlan, Sergio Aguero, Radamel Falcao a 2011, Diego Costa a 2012, Villa, daga nan Costa ya sake dawowa a 2014, sai Mario Mandzukic, Fernando Torres, Kevin Gameiro yanzu kuma ga Alvaro Morata.
-Manchester City: daga wancan lokaci tayi ƴan wasa irinsu Aguero, Adebayor, Mario Balotelli, Alvaro Negredo, Edin Dzeko, Carlos Tevez, yanzu kuma ga Leory Sane da Gabriel Jesus, amma babu wanda ya danne gurbin Aguero.
- Bayern Munich: yanzu zamanin Lewandowski ne, Lokacin da Benzema ya zo Real Madrid a 2009, Mario Gomez ne ke jagorantar ƙungiyar ta Munich, sannan Mandzukic ya zo daga Wolfsburg, amma lokacin da Robert Lewandowski ya sanya hannu daga Borussia Dortmund a 2015, komai ya canza.
- PSG: yanzu haka Mauro Icardi shine Tauraro, daga 2009 zuwa yanzu sunyi ƴan wasan gaba irinsu Guillaume Hoarau, da Peguy Luyindula, Gameiro, Ibrahimovic, Edinson Cavani, Mauro Icardi, sannan wasu lokutta sukanyi amfani da Mbappe a matsayin lamba 9.
-Juventus: daga 2009 zuwa yanzu sunyi ƴan wasan gaba irinsu Alessandro Del Piero, Mirko Vucinic, Tevez, Fernando Llorente, Mandzukic, Morata da Gonzalo Higuain sannan kuma ga Ronaldo wanda shima suke yawan amfani dashi a matsayin lamba 9.
-Liverpool: yanzu haka firmino ne ke jan ragamar ƙungiyar amatsayin lamba 9. Daga 2009 lokacin da Benzema yazo Madrid Fernando Torres ne a Liverpool, Suarez, Balotelli da Andy Carroll.
Chelsea: Werner shi ne sabon dan wasanta. Kafin nan anyi Didier Drogba, Fernando Torres, Morata, Michy Batshuayi, Costa, Olivier Giroud, Romelu Lukaku, Loic Remy yanzu kuma ga Timo Werner.
Idan ka ɗauki dukkanin wata ƙungiya dake nahiyar Turai zakaga Benzema shine striker ɗaya tilo da ya daɗe yana jan ragamar ƙungiya guda kuma yafi kowanne haskawa a wannan zamani a jerin ƴan ƙwallo masu yawan shekarun sa.
Yanzu haka shine lamba 9 daya tilo daya taɓa Jan ragamar ƙungiya guda ta lashe kofin nahiyar zakarun Turai har guda uku a jere.
Group Leader:
Lawan M Ahmad Karaye.
5 hrs · Real Madri

Post a Comment

0 Comments