Shin Menene Sakamakon Bincike da akeyi akan batun ɓatan Abubakar Dadiyata?


Gaskiya kama  wannan matashin da Akai ya tada mun hankali matuka wallahi, irin Yadda na saurarin jawabin Iyayinsa Abun ba dadi tausayi yakamani gaskiya, toh ba Abinda zamuce sai dai Allah ya kubutarda shi daga hannun miyagun mutane.
Wato Abun sai Adu'a kawai, dan Mulkin kama karya da akeyi a ƙasata Najeriya yayi yawa, baka da yancin yin magana sai abika da masifa, amma dukda hakan yazama dole mutashi tsaye dan kwatowa kanmu yanci a kasar nan, tsoro bazai kaimu ba.

A daidai wannan gaɓa zan ƙara janyo hankalin ƴan uwana matasa masu Rubutu akan sha'anin siyasar Najeriya dasu kiyaye harshen su, Kowa dai ya rubuta abun da ranar lahira zai iya bada amsa. Tunda Kaji Manzon Allah ( S.A.W ) Ya Nuna Harshensa Yace "Kuffa Alaika Haza" To Kasan Akwai Hikima Aciki, Harshe Bala'i Ne Idan Baka  Iya Kula Da Shiba. Mu ƴan Najeriya Ba Wani Abu Bane Yake Rudar Mu illa Wannan Kalaman Da Ake Cewa "Yanci  Fadan Albarkacin  Baki" Wato (Freedom Of Speech) Wanda Kuma Karya Ne babu shi a Najeriya, Tarko Ne Kawai Aka ɗanawa Mutane Domin Su Wadanda Zakayi Maganar Akansu Sunfi ƙarfin Ka Domin Suna Da Mulki, Suna Da Kuɗi, Sannan Kuma Basu Da Imani Idan Sukaga Kazame Musu Kadan Garen Bakin Tulu To Wlh Sai Sun Kawar Da Kai Tunda Baka Da Soja Baka Da Dan Sanda Sai Dai Harshe Wanda Zai Kai Ka Ya Baro Ka, Ada Idan Mutum Ya Taba Muhibbarsu Sai Dai Susa Aje Akamashi A Kulle To Yanzu Sun Canja Salo Kawai Sai Dai Aje Aduke Ka Kamar Wata Kaza A Rasa Inda Akayi Da Kai  Kirana Ga Matasa Sa Shine Duk Sanda Zakayi Magana Kayi Tunanin Kafin Kayi Ta Shi Kuma Wannan Bawan Allah Abubakar Dadiyata Allah Ya Bayyana Shi Albarkacin Annabi Da Alqur'ani, Ba'abinda ya gagari ubangiji, da waɗanda  suka kamashi da waɗanda suka saka akamashi, da shi wanda aka kaman, damu baki ɗaya duk muna ƙarƙashin ikon Allah. Allah maigirma da daukaka ga bawanka bawanda yasan inda yake sai kai, ba wanda zai iya kwatoshi sai kai, Allah ka kwato manashi kamarya dashi ga iyalansa ameen.

02/80/2020
Lawan M Ahmad Karaye

Post a Comment

0 Comments