a tsawon makwannin da aka yi ana cikawa, Minista Sadiya Umar Faruq ce ta bayyana haka yau Talata, tace an rufe website din shekaran jiya 09-08-2020.
Da ace za'a ce na bayar da shawara:
Da sai nace, tunda ance ana so a dauki mutane dubu dari hudu ne kawai.
Me zai hana a dauki mutane miliyan biyu, in yaso a dawo da kudin da ake bayarwa zuwa Naira dubu 20 duk wata, madadin dubu 30.
Saboda mutane da yawa su samu.
.
Amma lamarin ba zai yi tsari ba, idan aka ce an watsar da mutane miliyan hudu da dubu dari shida, an dauki mutane dubu dari hudu rak.
Idan aka dage da cewa lallai sai an dauki mutane dubu dari hudu rak acikin mutane miliyan biyar, toh gaskiya ba'a taimaki mutane ba, kuma ba'a yi tsari me kyau ba.
Ina ganin ya kamata gwamnati ta fahimci akwai bukatan ta kara bude hannu tare da Aljihun ta game lamarin N-POWER din nan.
Mafi karancin abinda za'a dauka a yanzu ya kamata ya zamo mutane miliyan daya da rabi ne, gaskiya kenan.
Mutane miliyan biyar hakan ya nuna akwai kalubale akan gwamnati.
.
Lallai gwamnati ta sake tunani akan adadin wadanda ada aka ce za'a dauka, sun yi kadan gaskiya.
Batun cewa za'a dauki mutane dubu dari hudu a barshi ma, a ajiye shi a gefe.
Batun daukan mutane miliyan biyu ko mutane miliyan uku ya kamata ayi.

0 Comments