me yasa kayan abinci yayi tsada ?

Me yasa kayan abinci yayi tsada, kuma yake kan yin tsadar, daga ina matsalar take?
Acikin wannan rubutun na bayyana wasu manyan dalilai guda shida (6) wanda sune dalilin tashin kayayyakin abinci, da kuma halin da mutane da dama suka samu kansu aciki.
1. Abu na farko da ya jawo wadannan tsadan a tsakanin al-umma shine dokar kulle tare da zuwan annobar cutar coronavirus a fadin duniya, wanda ya shafi kasar mu Nigeria da sauran kasashen.
.
Wannan dokar kulle itace kanwa uwar gamin hau-hawar kayayyaki a duk inda kaje a duniya, babu wata 'kasa a duniya da a yanzu mutane talakawa basa kukan tsadan rayuwa saboda kayan abinci yayi tsada.
A lokacin dokar kullen abincin mutane ya 'kara, kudaden mutane sun 'kare, wanda yayi ajiya duk ya 'karar da ajiyar sa, saboda dogon lokacin da aka dauka ana zaune ana ci ba tare da ana sake tarawa ba.
Wannan shine tushen wahalar da mutane suke ciki a yanzu, saboda idan kaje kasuwanni akwai abincin amma mutane basu da kudi.
.
A dai dai lokacin da ake cikin dokar kullen kuma gwamnoni da masu mulki suka fake da cewa ma'aikata basa zuwa aiki, dan haka suka ki biyan su hakkokin su, aka rike al-bashi da sauran su, bayan an gama dokar kullen kuma basu biya abinda suka rike na ma'aikata ba.
.
2. Abu na biyu da ya jawo tsadan kayan abinci sune 'yan kasuwa da manyan masu kudi, sun saya abinci sun tara, sun boye, idan suka fito dashi sai su ninka kudin sa sau biyu zuwa uku daga abinda suka saya a lokacin da abincin baida tsada.
Misali:
Wani 'dan uwa na yaje kasuwa ya sayi garin masara da safe akan Naira 270, da yamma sai wata mata tace garin ya mata kyau tana so aje a samo mata irin wannan, sai ya koma kasuwar da yamma wurin mutumin, sai yace masa gari Naira 290.
Daga safiya zuwa yamma Naira 20 ta 'karu, kuma Buhuhunan garin sun fi 30 a shagon sa.
Dan haka mu talakawan mune asalin mugayen da muke wahalar da 'yan uwan mu fiye da yadda masu mulki ke wahalar damu.
.
3. Abu na uku da ya jawo tsadan kayan abinci itace gwamnatin tarayya data gwamnatocin jihohi, ta yadda gwamnatocin suka ki bude rumbunan gwamnatin (Silos), aka ki sake abincin dake rumbun gwamnati dan jama'a su samu sauki daga kuntatawar 'yan kasuwa.
Dama yana daga cikin amfanin "Silos" idan gwamnati taga jama'a suna shan wahala da kayan abinci, sai ta bude nata ta sayar dashi da Araha domin talakawa su samu sauki daga hannun 'yan kasuwa masu mugunta.
.
Misali, gwamnatin tarayya tana sane da wannan tsadar kayan abincin, Ministan Noma 'dan Arewa ne, 'dan Kano ne, amma menene suka yi akan haka, kuma gwamnati tana iya sanin ga abinda zai faru nan gaba base on bincike tun kafin talakwa su sani, me aka yi dan saukaka wa mutane wannan?
Sannan daga 'bangaren gwamnati tallafin data bayar a bayar ma talaka ba'a bi sawun wadanda aka basu ba, an kyale su kawai, ba bincike ba bin diddigi, dan haka a wurin talaka 'daya ne da ba'a bayar ba.
.
Sannan wasu gwamnatin jihohi sun rike takin da manoma zasu amfana, an bar Manoma da 'yan kasuwa, taki yayi tsada a hannun 'yan kasuwa, babu yadda Manomi ya iya dole ya sayi na hannun su duk tsadar sa indai yana son noman.
Da ace gwamnonin sun sake takin da na kasuwar bai yi tsada haka ba.
Ya kamata ace takin yayi arha fiye da kowace shekara saboda halin da aka samu akai aciki.
.
Shugaban kasa dai yayi abinda ya kamata akan taki, ya hada kai da kasar Morocco tun 2018, anzo ana yin mai kyau a Nigeria, kuma ya dauki ikon batun takin ya bayar ma adalin gwamna, gwamnan Jigawa Badaru Talamis.
Amma duk da haka gwamnatin tarayya ta kyale gwamnonin suna cin karen su akan batun takin.
.
4. Abu na hudu da ya jawo tsadan kayan abinci sune manoma, manoma suna da laifi iri biyu:
Na farko zasu Noma abinci, su ajiye har shekara ta zagayo, suna ji ana wahala suja suyi shiru, zaka ga mutum ya fito da Masara yana sayarwa daga gidan sa, yana da buhuhuna sama da 'dari, yau sai kaji ya 'kara Naira 20, gobe ya kara Naira 30, jibi Naira 50.
Bai je ko'ina ya saro Kaya ba, bai sayo a wurin wani ba balle yace shima an masa 'kari ne, shiyasa ya ya kara, babu haka, suna cutar da jama'a.
.
Laifin manoma na biyu shine, galibin su idan gwamnati ta basu tallafin Noma sai su sayar, za'a bayar da taimakon taki ko injin Noma sai mutum ya sayar ya kashe kudin, yazo bakin hanya ya zagi Buhari.
A kusa dani aka zo aka kawo tallafin taki, ana saukewa a Mota dillalai suna sayewa, idan aka bayar wa mutum sai yace wane nawa zaka saya.
Mutane sun ki suyi amfani da tallafin ko rancen ko bashin yadda yadda ya kamata, amma su suke cewa Buhari bai yi komai ba.
.
5. Abu na biyar da ya kawo tsadan kayan abinci shine masu iko a kasa-kasa, wadanda ake basu hakkokin jama'a amma sai su karbo su rike, su cinye.
Ko kasan yanzu haka hukumar EFCC ta kama shugabannin kungiyoyin Noman shinkafa da Auduga da Noman Masara da Dawa da Shinkafa?
Saboda shugaban kasa Buhari ya bayar da Naira biliyan 40 tun a December 2019 akan suje su karba a hannun CBN su raba wa manoma dan amfanin daminan 2020, amma sun je CBN sun karba sun cinye kudin?
.
Wannan yana daga cikin abinda hukumar EFCC reshen jihar Kano tace shine ya jawo tsadan kayan abinci a wannan shekarar a fadin Nigeria, saboda wasu 'yan iska sun cinye kudin da talakawa fiye da miliyan goma zasu yi noma dashi a Nigeria.
'Yan uwan mu talakawa in sun damu iko sai su wahalar damu, su kuntata mana, galibin mu bamu da tausayi, bamu da rahama wa junan mu.
Gwamnati ta bayar mu karba mu hana 'yan uwan mu wanda mun san suna cikin wahala.
.
6. Abu na 'karshe daga cikin dalilan da suka jawo tsadan rayuwa shine, tsananin sabon Allah da yayi mana yawa, ga talauci da sabon Allah a cikin mu, ga wahalan rayuwa ga zina-zinace, ga tsadan kayan abinci ga Luwadi da Madigo.
Kashe mutane saboda neman duniya, tsafi, sihiri, duk acikin Musulmi ake wannan mummunar aikin, dan haka wahala dole ta sauka akan mu.
Allah ya kyauta.

Post a Comment

0 Comments