Jami'an Manara Zasu Gudanar Da Taron Horaswa Akan Yanda Za'a Sami Bashi Daga Babban Bankin Nijeriya.
A kokarin su na wayarwa mutane kai akan tsarin bada bashi karkashin shirin "Manaraabp", jami'an na Manara zasu zagaya wasu daga cikin jihohin Nijeriya.
Yayin ziyarar tasu zuwa jihohi zasu gudanar da taron horaswa ga mutane tsari da kuma hanyoyi da zasu bi wajen samun bashi marar kudin ruwa daga babban bankin Nijeriya (CBN).
.
A wata takarda da ta fitar ta hannun daraktan Jibwis Social Media na kasa Alh Ibrahim Baba Suleiman, kamfanin na Manara ta bayyana jihohi da zata ziyarta da kuma wadanda zasu jagoranci wayar da kan jama'a.
Ga jadawalin kamar haka:
1.YOLA
> jihohin da zasu hadu: BORNO, TARABA da kuma ADAMAWA.
>Ranar taro: 15/08/2020
> Jami'in horaswa: Mal Usman Idris Funtua
2. BAUCHI
> jihohin da zasu hadu: GOMBE, YOBE da kuma BAUCHI.
>Ranar taro: 18/08/2020
> Jami'in horaswa: Dr. Auwal Mustapha Imam
3. FCT
> jihohin da zasu hadu: NIGER, BENUE, NASARAWA, KOGI da KWARA.
>Ranar taro: 22/08/2020
> Jami'in horaswa: Mal Usman Idris Funtua
4. SOKOTO
> jihohin da zasu hadu: KEBBI, ZAMFARA da KEBBI
>Ranar taro: 24/08/2020
> Jami'in horaswa: Dr. Auwal Mustapha Imam
5. KANO
> jihohin da zasu hadu: KATSINA, KADUNA JIGAWA da KANO
>Ranar taro: 27/08/2020
> Jami'in horaswa: Mal Usman Idris Funtua
6. IBADAN
> jihohin da zasu hadu: OGUN, OSUN, ONDO, EKITI da LAGOS
>Ranar taro: 30/08/2020
> Jami'in horaswa: Dr. Auwal Mustapha Imam
7. PORT-HARCOURT
> jihohin da zasu hadu: ENUGU, IMO, ANAMBRA, RIVERS, DELTA, CROSS RIVER
>Ranar taro: 01/09/2020
> Jami'in horaswa: Dr. Auwal Mustapha Imam
Mahmud Isa Yola,
National Publicity Secretary Jibwis Social Media Nigeria.

0 Comments