Ko jam'iyyar APC zata iya sake shiga sabon zaben jihar Bayelsa, duk da cewa kotun 'koli (Supreme Court) ta kore ta?
Yau Litinin, kotun sauraren karan zaben gwamna a na jihar Bayelsa ta soke zaben gwamna Duoye Diri na PDP, kuma ta bada umarnin a sake gudanar da sabon zabe nan da kwanaki 90 masu zuwa (idan Allah ya yarda), idan ba'a manta ba anyi zaben gwamna a jihar ta Bayelsa ranar 16 ga watan November 2019, inda jam'iyyar PDP ta lashe zaben da gagarumin rinjaye.
.
Ana cikin shirin gobe za'a rantsar da Mista David Lyon na APC sai kotun 'koli ta soke zaben sa, saboda an samu mataimakin sa a takaran da laifin takardun makaranta na bogi, wanda sunayen sa suka sha bam-ban a takardun karatun sa.
Sai kotun tace da wanda yaci zaben gwamna da mataimakin sa duk sun fadi, ba su za'a rantsar ba, a rantsar da dan takaran PDP, haka kuwa aka yi, PDP ta karbe jihar duk da cewa APC ce taci zaben.
.
Jam'iyyar ANDP sai ta shigar da 'kara cewa hukumar zabe INEC bata saka sunan ta da Logon ta a zaben ba, abin nufi ba'a saka sunan jam'iyyar ANDP da Logon ta akan ballot paper ba, dan haka a yau sai kotun tayi nazari akan haka, kuma ta yanke hukunci cewa ta soke zaben gwamnan Bayelsa, wanda yake kai a yanzu na PDP, kuma tace a sake sabon zabe nan da kwanaki 90.
Domin a bayar da dama wa jam'iyyar ANDP ta fafata ita ma.
Sai dai abin tambayar shine, shin ko APC tana da hurumin shiga zaben da za'a saken?
.
Masana harkokin shari'a da Lauyoyi suna ta bayyana fahimtar su, wasu suna cewa APC tana da damar shiga, wasu suce a'a APC bata da ikon shiga zaben.
Amma magana mafi inganci shine APC tana da ikon shiga zaben a nazarin da nayi (Abdul-Hadi Isah Ibrahim), amma idan har APC tayi 'dayan abubuwa biyu.
1. Idan ta canza 'dan takaran ta na mataimakin gwamna, ta kawo wani wanda baida matsala a takardun karatun sa.
.
2. Ko kuma shi mataimakin yaje ya gyara takardun karatun sa, ya gyara inda yake da matsala, yayi hakan kwanaki 45 kafin zaben da aka ce a sake (Base of the electoral act provision).
Idan suka yi 'daya daga cikin wadanda toh zasu iya shiga a fafata dasu a sabon zaben da kotu tace ayi.
.
Dalilin kuwa shine (Supreme Court helping), irin haka ta taba faruwa a jihar Bauchi, a shekarar 1999, Ahmadu Adamu Mu'azu ya tsaya takaran gwamna a jam'iyyar PDP, tare da mataimakin sa, kuma suka ci zaben, suka kayar da jam'iyyar APP ta Baba Ajiya (Allah yaji kansa).
Nan take jam'iyyar APP ta shigar da kara cewa ai mataimakin 'dan takaran PDP yana da matsala a takardun sa na makaranta.
.
Dan haka kotun koli ta yanke hukuncin cewa zaben Adamu Mu'azu rusasshe ne, ta soke zaben, mataimakin sa yaja masa, saboda Ticket din da suka yi takara Ticket ne na Hadaka, wato "Joint Ticket", duk abinda ya shafi 'daya toh dole zai shafi 'daya 'dan takaran, kotun tace a sake sabon zabe.
Nan take jam'iyyar PDP a wancan lokacin ta canja 'dan takaran ta, kuma ta shiga sabon zaben.
.
Kuma taci zaben, Adamu Mu'azu yayi mulki a jihar Bauchi har na tsawon shekaru Takwas, ya kammala a 2007.
Hukuncin da kotun tayi a yau, ba tana magana akan cigaba da zaben 2019 bane, a'a sabo ne, shiyasa ta Kira shi da "Fresh Election" kamar yadda Electoral Act ma ya bayyana, da ace "rerun" ne to da APC bata da ikon shiga.
Amma ba re-run bane, ba bye election bane, fresh ne, dan haka APC tana iya shiga.
.
Dan haka duba da hukuncin Supreme Court a 1999, game da zaben jihar Bauchi, yana halatta ma APC ta shiga sabon zaben da za'a yi nan gaba a Bayelsa idan ta cika wadancan , ka'idojin dana zayyana a sama.
.
Saboda wani lokaci hukuncin manyan kotuna, musamman Supreme Court yana zama doka, abinda muke cewa "Case Law".
Hukuncin da kotun tayi akan wani case, toh wannan hukuncin yana iya zama doka wani lokaci, sannan sauran kotunan kasar suna iya kafa hujja da hukuncin ta su yanke hukunci, idan an tambaye su dalili ba lallai su kawo ayar constitution ba, ba lallai su kawo ayar electoral Act ba, ko Penal Code ko Criminal code ba, suna iya kawo hukuncin Supreme Court a a matsayin hujjar su.
Abdul-Hadi Isah Ibrahim.


0 Comments