jijiyoyi uku masu matukar amfani jikin mutum

Likitoci masu bincike, da kuma masana bangarorin jikin 'dan Adam, da jijiyoyin jiki mutum, tun fiye da shekaru 'dari da suka wuce, suka ce sun gano cewa, a jikin zuciyar 'dan Adam akwai wasu manyan jijiyoyi wadanda suke da alaqa da wurare uku a jikin mutum. 1. Jijiya ta farko tana da alaqa da zuciya da Kwakwalwar 'dan Adam. 2. Jijiya ta biyu tana da alaqa da numfashin da mutum yake yi. 3. Ta uku tana da alaqa da motsin gabobin 'dan Adam. . Suka ce, a lokacin da 'dan Adam yazo zai mutu, sai wadannan jijiyoyin su fara jijjiga, da motsi mai karfi daga cikin zuciyar sa, wani lokaci har jijjigar ta fito waje sai aga gabobin mutum suna jijjigan suna (shaking), a lokacin da rai zai fita. Shiyasa zaka ga hatta dabba, Rago ko Saniya ko Kaza idan aka yanka su, zaka ga suna jijjiga, suna motsi mai karfi, saboda wadannan jijiyoyin suna jijjiga daga ciki, har jijjigar ta bayyana ta waje akan gabobin su. . Amma a lokacin da 'dan Adam ya mutu jijiyoyi biyu ne kawai zasu daina aiki, guda daya zata cigaba da aiki har bayan mutuwar sa, har lokacin da za'a saka shi a kabari. Jijiyar da zata cigaba da aiki itace jijiyar da take da alaqa da kwakwalwar sa da zuciyar sa. Amma jijiyar numfashi zata daina aiki, jijiyar motsin gabobin zasu daina aiki, jijiyar kwakwalwa ce kawai zata cigaba da aiki har bayan ransa ya fita. . Wannan aikin da jijiyar kwakwalwa take yi bayan mutuwar mutum shine dalilin da yasa mutum ya mutu amma yana jin abinda ake yi, kawai ba zai iya motsi bane, kuma ba zai iya numfashi ba, amma yana jin duk abinda ake yi, har a saka shi a ramin kabari. Shiyasa kaji manzon Allah (S.A.W) a Hadisin Bara'u Bin Azif (wani dogon Hadisi mai yawa, na fassara shi da hausa a wurin karatu na a masallaci). . Acikin hadisin manzon Allah yace "Mamaci yaja jin takun takalman mutane a lokacin da suke fita daga makabarta idan sun juya zasu tafi su bar shi". Malamai suka ce, tun ba yau ba Allah ya sanar da manzon Allah wannan ilimin, cewa wanda ya mutu yana jin me ake yi, saboda jijiyar kwakwalwar sa tana aiki har a lokacin da ya mutun. Daga cikin Hadisin Bara'u Bin Azif sai manzon Allah yace "Sannan kuma bayan an saka mutum a kabari sai a dawo masa da ransa gan-gar jikin sa". . Da wannan ne masana suka ce za'a dawo masa da aikin jijiyar numfashi da gabobi, dama jijiyar kwakwalwa tana aiki, sai ya amsa tambayoyin kabari, bayan an gama masa tambayoyin kabari sai a dakatar da dukkan jijiyoyin guda uku, na numfashi, dana kwakwalwa dana gabobi, sai ya fuskanci al-amuran lahira Kuma (Allahu Akbar). . Shiyasa a wani Hadisi zaka ji manzon Allah yace: "Karya kashin mamaci (Bones) hukuncin sa 'daya da karya shi a lokacin da yake raye". . Indirectly wannan Hadisin yana nuna maka idan ka karya kashin mamaci yana jin zafi kamar yadda zai ji idan da yana raye, shiyasa aka ce in ka karya mamaci zunubin ka kamar ka karya wanda yake raye. Daga 'karshe, ba dan kar rubutun yayi yawa ba da na kammala wannan bayanin sosai, a hakan na tsallake wasu gabobi na bayanin. Amma a takaice, Turawa da masu bincike suka ce, da ace jijiyar numfashi zata yi aiki amma jijiyar gabobi dana zuciya su tsaya, suka ce da zasu iya tayar da wanda ya mutu. . Amma ilimin su ya gagara sanin yadda za'a tsayar da jijiyar numfashi ta cigaba da aiki a lokacin fitar rai, shiyasa ba zasu iya dawo da mutumin da ya mutu ba. Allahu Akbar...... Wani lokaci in sha Allah, nan gaba zan mana rubutu akan yadda za'a tashi a kabari, tare da wasu bincike da aka gano jijiyar da zata fara aiki a jikin mutum yayin Busan Kaho, yayin tashi daga Kabari. Abdul-Hadi Isah Ibrahim

Post a Comment

0 Comments