abubuwa goma da dole saika daina tsoro kafin fara sana a

ABUBUWA GOMA DA DOLE SAI KA DENA TSORO KAFIN KA FARA SANA’A

Mene ne marabar wanda yanzu haka a lokacin nan da nake wannan rubutun yake samun riba, yana mayar da canji cikin aljihu da ragowar ku wadanda kullum zaku tashi daga bacci, sannan ku koma ku kwanta da dare ba tare da samun ko kwandala ba?
Tsoro.

Ko sau nawa mai son yayi sana’a ya tabbatar wa kanshi abunda yake da niyyar yi. Karanta wadannan abubuwa goma da duk wani mai so ya fara sana’a yake tsoro da hanyar shawo kan su.

1. RASHIN SANIN DAGA INDA ZA A FARA

Yawancin masu so su fara sana’a, basu san daga inda zasu fara ba bayan yanke shawarar hada-hadar da suke son yi. Ka fara da neman wani wanda ya cimma sak irin burin da kake son cimmawa.
Yi bincike akan wannan mutum, da irin kasuwancin sa sannan ka tuntubi shi ka gani ko zai iya baka shawara da bayanai. Idan bashi da lokaci ko sha’awar yayi maka magana, to zaka gane cewa ya samu nasara, kuma kaima zaka iya.
Ka cigaba da gashi sannan kayi abunda ya fi mayar da hankali, kana cigaba da tafiya, hanyar na kara maka haske.

2. RASHIN KWAREWA

Ta yiwu ka san abubuwa da yawa akan hajjar ka ko sana’ar ka domin amsa duk wasu tambayoyi da kwastomomi zasu yi maka, da ma warware musu duk wasu matsaloli da ka iya tasowa. Saboda haka kar ka damu kanka idan kana ji kamar baka son komai a wannan fannin ba.
Dangane da abubuwan da baka sani ba, zaka iya samo amsoshi. Babu kunya wajen neman ilimi. Maganar gaskiya, wannan abu ne ma da ya kamata ka ringa yi kullum idan kana so ka cigaba, komai girman sana’ar ka. Baza ka taba dena koyo ba: Ka saka rigar kwararre sannan ka sadaukar da kanka wajen tabbatar da sana’a mai burgewa.

3. ANA MAKA KALLON MARA HANKALI

Mutane da yawa zasu yi maka kallon mara hankali a lokacin da kake fara sabuwar sana’a, kuma gaskiya suka fada. Abu mafi sauki na yi shine kar ka taba daukar kasada, ka je ka yi ta yi wa wani aiki har karshen rayuwar ka.
Ya ka ji a ranka dangane da abun da na rubuta yanzu?
Nasir NK Young Entrepreneur
(NKTREDER FOUNDATION)

Post a Comment

0 Comments