NASAN ZAKA TAUSAYAMA SADIYA IDAN KAJI LABARINTA.


Sadiya Itace macen da Nafi Tausayi Cikin Matan dana Taɓa Haɗuwa dasu a rayuwata. Labarin Sadiya labari ne mai tsayi, mai ban mamaki da kuma ban Tausayi. Sadiya ƴar Asalin jihar Bauchi ce, amma mun haɗu ne a jihar Lagos shekaru 2 da suka gabata kasancewarta maƙwabciya a wajen da nake, tana yawan kawo min ziyara muyi ta hira.

Kwanci tashi zumuncin mu ya girmama har takan aiko min da ruwa, Lemo, etc sai nake gayama wani abokina irin kirkin Sadiya da irin kyautatawar da take mini, sai yake cewa dani "sona take yi" ya kamata na cigaba da bata kulawa. Bayan mun amince da juna soyayya tayi nisa, Wata rana muna hira da Sadiya sai take cewa dani "inaso na faɗa maka wata magana amma dai ina tsoron kada ka gujeni" sai nake cewa da ita kawai ta faɗa mini ko menene, sai take cewa dani "ita gaskiya ba zata faɗa mini ba sabida tasan cewa indai ta faɗa min zan guje ta" data fahimci raina ya ɓaci sai take cewa dani "lokaci baiyi ba". Nan na dinga tunane-tunane da saƙe-saƙen ko menene Sadiya take ɓoye mini? Bayan kwana biyu sai na matsa mata saita faɗa min, sai take cewa "Na yarda zan faɗa maka amma sai kayi mini alƙawarin ba zaka gujeni ba, sabida ina tsoron kasan Sirrina daga bisani ka gujeni kuma ka dinga kallona da abun" sai nake cewa da ita a gaskiya bazan iya yi miki alƙawarin cewar bazan gujeki ba a sakamakon bansan irin abunda ke tattare dake ba ko yakai matsayin da ba kowane zai iya kasancewa dake ba.

Kawai saita fara bani labarinta kamar haka: "Na taso a wannan gari na Lagos, Mahaifina a wannan gari yake kasuwanci sama da shekaru 30, daga bisani saiya ɗaukomu daga jihar Bauchi muka dawo nan da zama, a bisa al'adar family ɗinmu idan za'ayi miki aure kawai za'a zaɓar miki wanda zaki aura ne a cikin dangi, lokacin na gabatowa za'a gaya miki ga wanda zaki aura, kawai a sanya rana ayi biki a watse" itama haka akayi mata tun tana ƙarama, mijin ya dinga wahalar da ni daga bisani aurenmu ya rabu, yanzu dai ni bazawara ce. Bugu da kari al'adar gidanmu ba'a saka yan mata a Makarantar boko koda firamare ba'a barin mace tayi a gidanmu, sabida mahaifinmu baya so, tun ana basa shawara ya riƙa saka ƴaƴansa mata harma an daina.

Sai tace dani, Itafa a gaskiya ta kamu da sona ne kuma burinta shine muyi aure, amma saidai tasan abune mai wahala, a sakamakon ni mazaunin Kano ne ita kuma Lagos, gaskiya bata tunanin iyayena zamu amince da wannan batu, sabida hakan ta taɓa faruwa da ita a baya lokacin da wani saurayi yace yana Sonta da aure, amma data faɗa masa ita bazawara ce saiya guje ta, itama tasan cewar bazan aureta ba, amma na sani tana ƙaunata domin Allah. Ni kaina saida na shiga cikin tunani a sakamakon shigowa cikin rayuwata da tayi, da kuma irin halinda ta shiga. Daga nan sai tace dani kawai na manta da batun soyayya kawai na ɗauke ta amatsayin ƴar uwa kamar yadda ta ɗaukeni kuma tana bukatar shawarwari na a koda yaushe.

A kullum Sadiya tana faɗamin cewa "Ni Kano tana burgeni, babban burina shine nayi aure a Kano" ni kuma sai na dinga mata fatan alkhairi. Kunsan meke faruwa a halin yanzu? A ƙarshe dai Burin Sadiya ya kusan cika nayin Aure a jiharmu Kano, Allah ya kawo mata wani wanda zata aura a Kano, yanzu saura kwanaki 20 ayi Auren ta.

Na yaba da ƙyawun Sadiya, hankalin ta, da kamarta. A haɗuwa ta da Sadiya na koyi abubuwa da dama daga gareta sannan na ƙara fahimtar irin ƙalubalen da mata suke fuskanta a wannan zamani musammman faɗawa a tarkon mayaudara da wasu gurɓatattun majaje keyi, Har ila yau zaɓama Budurwa mijin Aure kamar yadda aka yima Sadiya tun tana ƙarama abune wanda muslinci ya amince dashi amma idan ka killace ƴarka ka bata tarbiyya ta Sunnah hakane zaisa ka iya sarrafa ƴaƴanka kuma ka aurar dasu ga mijin daya dace babu illa a ciki, saidai Sadiya tayi rashin sa'ar miji. Sannan na fahimci irin halin da mata suke faɗawa Idan suka faɗa tarkon yaudara.
A ƙarshe ina yima Sadiya fatan alkhairi, Allah kasa wannan Aure ya tabbata, ya kuma sa wannan mutum ya riƙeta riƙo na mutunci da ƙyautatawa.

17/07/2020.
Lawan M Ahmad Karaye

Post a Comment

0 Comments