Da farko Dai ina Mai miƙa saƙon jajantawa ga ƴan uwana mutanen arewacin Najeriya bisa irin Kisan kiyashi dakuma zubar da jinin mu da ƴan ta'adda Ke yi ba dare ba Rana.
Idan Na zauna ina nazari dangane da yadda waɗanannan abubuwa Ke faruwa nakan kasa gane Babbar matsalar Daga ina take fitowa tsakanin shugaba Muhammad Buhari dakuma masu ruwa da tsaki a Fannin tsaron ƙasar nan.Shugaba Muhammad Buhari ya damƙa wa al'ummar arewa dukkanin wata ragamar tsaro ta ƙasar nan Amma abin mamakin saiga arewan Na ta fama da matsalolin kashe-kashe dakuma zubarda jinin Al'ummar da Basu jiba Basu Gani ba Musamman ma jahar Katsina a yanzu wacce Shugaban ƙasar yafito Daga cikinta.
A yanzu haka arewacin Najeriya Nada kaso mafi tsoka a harkar tsaron ƙasar Kamar Yanda Zan lissafo muku ku Gani a cikin wannan rubutu:-
-Commander in chief of army forces, Muhammad Buhari Daga jahar Katsina.
-Shugaban sojojin ƙasa-Laftanal Kanal Tukur Yusuf Buratai Daga jahar Borno.
-Shugaban sojojin Sama-Air Marshall Sadiq Abubakar Daga jahar Bauchi.
-Shugaban Hukumar ƴan Sanda- Muhammad Adamu Daga jahar Nasarawa.
-Shugaban Hukumar tsaro ta farin Kaya(DSS),Yusuf Magaji Bichi Daga jahar Kano.
-Shugaban Hukumar civil defence-Alhaji jimada Gana Daga jahar Niger.
-Ministan tsaro-Bashir Magashi Daga jahar Katsina.
-Mai Bada shawara akan sha'anin tsaro-Babagana monguno Daga jahar Borno.
-Chiyaman kwamatin tsaro a majalissar dattijai-Aliyu Wamakko Daga jahar Sokoto.
-Chiyaman kwamatin a majalissar dattijai ɓangaren sojojin ƙasa-Ali Ndume Daga jahar Borno.
-Chiyaman kwamati a ɓangaren sojin sama-Bala ibn Na'Allah Daga jahar Kebbi.
Kai tsaye Bazan iya ɗora wannan alhaki ga shugaba Muhammad Buhari ba haka zalika Suma masu ruwa da tsaki a Fannin tsaron ƙasar Amma Kuma dole akwai Mai wannan laifin.
Idan Har shugaba Buhari yasan Basu dace ba aka Basu amanar tsaron ƙasar nan to tabbas yaci amanar mu,Sannan Idan Kuma Suna sane ake wannan aika-aikar to tabbas sunci amanarsa.
Kaso 50% Daga cikin ɗari na jama'ar da suka zabi Shugaban ƙasa Muhammad Buhari a arewa sun zabeshi Domin magance matsalar tsaro da ya addabi yankin Na arewa a wancan lokaci,Sai kuma Kash! Mutanen arewacin sunga akasin hakan.
Daga Idris Ya'u Krj
Fatana shine Allah Ubangiji ya karkato da hankulan manyan ƙasar nan su Duba yanayin da tsaron da arewacin Najeriya Ke ciki.
0 Comments