Shin arewa riba ko faɗuwa?



Tun dawowar Mulkin dimukuradiyya a Nigeria a 1999 Arewacin Nigeria yake tafka asara a hannun 'yayanta.

Manyan Arewa su suke rike da akalar Nigeria tun bayan juyin mulkin 1966 wanda a zahiri bai yi nasara ba har izuwa 1999 lokacin da suka dauki mulkin kacokan suka damkawa kudu da gurgun tunani biyu cewa zasu iya juya wanda suka dora kuma zai kare musu muradunsu, sun manta da karfin kujerar tare da cikakkiyar damar da duk wanda yake kanta sai yadda ya dama haka za a sha.

Obasanjo yayi amfani da damar da suka dade suna nema ya taimaki yankinsa sosai,ya samar musu da cikakkiyar wutar lantarki, ya habbaka harkar noma da kiwo, ya basu rancen kudade masu kauri da dai abubuwa masu dama na raya al'umma, a daidai lokacin da ya hada kai da yan Arewa ya karyata.

Ya fara da Kano, inda aka hanamu wutar lantarki, sandiyyar da tasa kamfanoninmu suka mutu suka zama kangwaye a Sharada da Bompai, ma'aikatan suka rasa aiki, da yawa suka koma shaye-shaye da sace-sace.

 Ya dakatar da aikin janyo teku wanda Gen. Abacha ya faro, ya tilasta amfani da rogo maimakon alkama ddss, uwa uba ya zabawa kansa magajin da yasan bashi da koshin lafiyar da zai iya jan ragamar, ya kuma hadashi da wanda yake so ya ja ragamar.

Haka marigayi Umaru M. Yar Adua yazo, ya dawo da aikin jawo teku da kokarin farfado da harkar noma, inaa! Jikin yayi rauni, har ta Allah ta kasance.

Jonathan ya hau ya soke aikin janyo teku ya mai da kudin aikin Niger delta aka ba da su ga 'yan ta'addan Niger delta su karo karatu a jami'o'in waje.

Ya soke duk shirin Umaru na 7points agenda, ya bawa yan ta'addan Boko haram dama suka ci karensu ba babbaka, suka hargitsa Arewa, suka talautata, suka kashe, suka sace suka kona Arewa, kaso mai yawa na 'yan Arewa suka zama 'yan gudun hijira, kasuwanci ya lalace, duk muka dimauce.

Da bala'i yai bala'i sai muka tuno maganar Malam Aminu kano (Nigeria kasa dayace, amma kowa da gidan ubansa) sai talakawa suka saka General Muhammadu Buhari a gaba.

Post a Comment

0 Comments