Allahu Akbar......
Idan ka lura da Surorin Al-qur'ani mai girma daga Surah ta farko (1) itace Suratul Fatiha, Surah ta biyu itace Baqarah, idan kazo dai dai Surah ta goma sha shida (16) zaka ga sunan ta Suratun Nahli, abinda ake nufi da Nahl itace 'Kudar Zuma ko "Bee" da Turanci, idan ka lura da kyau zaka ga Surar tayi magana akan 'Kudar Zuma, wanda zaka yi mamakin sakamakon da zamu fitar maka daga wannan Surar da kuma binciken Science na wannan zamanin.
.
Binciken Turawa da masana ilimin kimiyya ya tabbatar da cewa 'Kudar Zuma tana "16 Chromosome", abin nufi shine "sinadarin dake haduwa ya samar halittar 'kudan zuma guda goma sha shida ne", idan ka lura Surar da tayi magana akan 'kudar Zuma itace Surah ta 16, Chapter 16.
.
Binciken su ya tabbatar da cewa acikin kudar Zuma akwai namiji, da Turanci ana ce masa "Drone", shima yana da 16 Chromosome, kamar yadda Suratun Nahli itace Surah ta 16 "The Bee".
Har wa yau, binciken da masana suka yi a jami'o'i da dama a fadin duniya ya tabbatar da cewa akwai nau'in kalar kudar zuma har guda 16 a fadin duniya, babu na na Sha bakwai.
Yanzu ka kara gane hikimar data sa Suratun Nahli itace ta sha shida?
.
Binciken masana kimiyyar ya tabbatar da cewa "Bee's Eggs" Kwan 'kudan zuma yana farawa ne daga rana ta 'daya zuwa rana ta goma sha shida (in 16 days), ka lura cewa ba a banza aka saka Suratun Nahli a lamba ta 16 ba ko acikin Al-qur'ani?.
Wani binciken kuma ya bayyana cewa kudan Zuma sukan rayu tsawon kwanaki 120 zuwa 128, kaga 128 sune adadin yawan Suratun Nahli.
A takaice dai Zuma takan bata yin fiye da kwanaki adadin yawan ayoyin Surar.
Allahu Akbar.......
.
Wani bincike da Masana suka yi a shekarar 1995 ya tabbatar musu da cewa kudar Zuma akwai namiji akwai mace, suka ce binciken su ya gano cewa macen kudar Zuma itace take samar da ruwan zuma "Honey", namijin baya samar da ruwan zuwa, wannan binciken tun tunin yana cikin Suratun Nahli, ayah ta 68 zuwa ta 69, Allah yace:
:
ﻭَﺃَﻭْﺣَﻰ ﺭَﺑُّﻚَ ﺇﻟَﻰ ﺍﻟﻨَّﺤْﻞِ ﺃَﻥِ ﺍﺗَّﺨِﺬِﻱ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺠِﺒَﺎﻝِ ﺑُﻴُﻮﺗًﺎ ﻭَﻣِﻦَ ﺍﻟﺸَّﺠَﺮِ ﻭَﻣِﻤَّﺎ ﻳَﻌْﺮِﺷُﻮﻥَ * ﺛُﻢَّ ﻛُﻠِﻲ ﻣِﻦ ﻛُﻞِّ ﺍﻟﺜَّﻤَﺮَﺍﺕِ ﻓَﺎﺳْﻠُﻜِﻲ ﺳُﺒُﻞَ ﺭَﺑِّﻚِ ﺫُﻟُﻼً ﻳَﺨْﺮُﺝُ ﻣِﻦ ﺑُﻄُﻮﻧِﻬَﺎ ﺷَﺮَﺍﺏٌ ﻣُّﺨْﺘَﻠِﻒٌ ﺃَﻟْﻮَﺍﻧُﻪُ ﻓِﻴﻪِ ﺷِﻔَﺎﺀٌ ﻟِّﻠﻨَّﺎﺱِ
:
"Kuma Ubangijin ka yayi wahayi (na ilhama) zuwa ga 'kudar Zuma, cewa ki riki duwatsu a matsayin gidan zaman ki, da kuma Bishiyoyi (kiyi gida, Kango a jikin su) da kuma wurin da suke rayuwa (jikin gidajen mutane), sannan sai kici daga dukkan 'ya'yan itace (tsirrai) sannan ki shiga tsarin da Ubangijin ki yayi miki ki wuce, (zumar) tana fitarwa daga cikin ta (Stomach) wani irin abun sha mai launi daban daban (different colors).....".
(Jar saka, farar saka, bakar saka, duk Zuma tana yi).
.
Research din su yace macen ce take samar da ruwan zuma, ba namiji ba, yanzu ka lura da cikin wannan ayar da na kawo, kamar haka
.
Idan ka lura acikin wannan ayar da na kawo sai Allah yace ﺛﻢ ﻛﻠﻲ "Summa kuliy" wannan sigar macece a Larabci, idan namiji ne ba za'a ace "Summa kuliy" a ayar ba.
Sai Allah yace ﻓﺴﻠﻜﻲ "Fas lukiy" wannan da female gender Allah yake magana, ba namiji ba.
Sannan Allah yace ﺳﺒﻞ ﺭﺑﻚ wannan ma sigar mace ce.
Sannan Allah yace ﺑﻄﻮﻧﻬﺎ "Buduni ha", cikin ta, wannan sigar macece ba namiji ba.
Kenan Al-qur'ani ya tabbatar mana cewa macen kudar Zuma itace take samar da ruwan zuman me zaqi wanda ake sha.
(Wannan Al-qur'anin dake hannun ka, ka zuba masa ido kawai, abubuwan dake cikin yafi karfin tsarawan 'dan Adam).
.
Sannan idan ka lura Surar tana da ayoyi 128 ne, idan ka raba shi gida biyu zai baka 64
Wato 128 ÷ 2 = 64
Idan ka lura acikin Surar (wato Suratun Nahli 'din) zaka ga akwai ayoyi guda 64 wadanda suke dauke da Sunan Allah acikin su "Allah", sannan akwai ayoyi 64 wadanda babu sunan Allah acikin su.
.
Sannan idan ka lura yawan ayoyin Surar 128 is a multiple of 16.
Idan ka buga 16 sau 8 zai baka 128.
Abu na 'karshe, idan ka lura acikin wancar ayar dana kawo , Allah yace:
"Sai ki ci dukkan itace ko ganye".
Wannan zahiri ne, babu wani ganyen da kudar zuma bata cin furen sa ko ganyen sa.
Tana cin mai 'daci, mai Zaki, mai bauri, mai tsami, mai wari, Mai kamshi duk tana ci, kamar yadda Allah ya fadi a ayar, taci kowanne.
Dan haka duk abinda ka gani a Al-qur'ani haka yake a zahiri, sai dai binciken mutane ya kasa ganowa.
.
Acikin Suratul Fussilaat, Allah yace:
ﺳَﻨُﺮِﻳﻬِﻢْ ﺁﻳَﺎﺗِﻨَﺎ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺂﻓَﺎﻕِ ﻭَﻓِﻲ ﺃَﻧْﻔُﺴِﻬِﻢْ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺘَﺒَﻴَّﻦَ ﻟَﻬُﻢْ ﺃَﻧَّﻪُ ﺍﻟْﺤَﻖُّ
"Da sannu a hankali nan gaba za mu yi ta nuna musu ayoyin mu acikin sammai da kassai, da kuma jikin su, har sai ya bayyana musu cewa shi (Al-qur'ani) gaskiya ne".
Suratul Fussilaat ayata 53.
0 Comments