Wani bincike da Turawa masana ilimin kimiyya suka yi game da duniya, ya bayyana musu cewa wannan duniyar da muke cikin ta akwai ruwa da 'kasa, ruwan ya kai kashi 71.1111 a fadin duniyar nan, sai 'kasa kuma ta kai kashi 28.8888, wannan research din sun yi shi shekaru 69 da suka wuce, sai dai abinda zai baka mamaki da Al-qur'ani mai girma shine abubuwan da zan kawo maka a kasa, wanda zaka gani
.
Idan ka lura acikin Al-qur'ani zaka ga kalmar “Bahr” wato Kogi (Ruwa) ko (water) an ambaci kalamar har sau 32 acikin littafin Al-qur'ani mai girma.
Abu na biyu idan ka lura zaka ga kalmar "Al-ard” ko "Barri" wato 'kasa ko (Earth) an ambace ta sau 13 acikin Al-qur'ani.
.
Idan ka hada yawan kalmar Ar-dh da kalmar Bahr, zai baka = 45.
Wato 32 + 13 = 45.
.
In details, sai kace
“water = 32 times + “earth” = 13 times = 45 times).
Idan ka hada su duka 32 da 13n zaka ga an ambace su sau 45 kenan a Al-qur'ani.
Yanzu ka lura da wannan
Ka buga wannan da calculator dinka:
32 yawan adadin kalmar (Kogi) a raba shi da yawan adadin Kogi da 'kasa sau 'dari,
Wato
32 / 45 × 100%
Zai baka 71.1111%
Wannan shine yawan adadin yanda ruwa ya kewaye duniya, wato ruwa yafi 'kasa yawa da kashi 71 cikin dari.
.
Gashi a takaice da Turanci:
(Number of “bahr” (water) divided by the total number of words “earth+water”, multiplied by 100% gives:
(32 / 45 ) x 100 = 71,1111%
.
Na biyu sai batun yawan adadin kasa a doron duniya:
Sai kace, yawan adadin kalamar 'kasa acikin littafin Al-qur'ani wato 13, a raba shi da 45 (yawan adadin kalamar 'kasa da ruwa acikin littafin Al-qur'ani) sau 'dari, zai baka 28,8888%.
Wato : (13 / 45) x 100 = 28,8888%
.
Gashi a takaice da Turanci
The total of words “barr and Ard” (earth) divided by the total number of words “earth+water”, and multiplied by hundred, equal to 28,8888%
Wannan shine adadin yawan filin da kasa ta kewaye na fadin duniyar da muke cikin ta.
Dan haka wannan binciken da suka yi bai ci karo da Al-qur'ani ba (Qur'anic Mathematic).
ﺃَﻓَﺴِﺤْﺮٌ ﻫَﺬَﺍ ﺃَﻡْ ﺃَﻧْﺘُﻢْ ﻟَﺎ ﺗُﺒْﺼِﺮُﻭﻥَ
"Shin wannan Al-qur'anin sihiri ne, ko kuma kune baku gani?".
Suratuz Zaariyaat, ayah ta 17.
.
"Ka fada musu da ace mutane da Aljanu zasu hadu domin su zo da wani littafi irin wannan Al-qur'anin!!! kace musu ba zasu iya ba (har abada) koda sashen su yana taimakawa sashe".
Suratul Isra'i, ayah ta 88.
Chapter 17 verse 88.


0 Comments