Tun Bayan lashe gasar cin kofin nahiyar zakarun Turai (UEFA champions league) karo na 8 da Real Madrid tayi a shekarar 2000 data lallasa Valencia daci 3_0 ne magoya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa suketa faman cece-kuce a sakamakon ta zarta kowacce ƙungiya a duniya lashe gasar tun a wancan lokacin, inda magoya bayan sauran ƙungiyoyi ke ganin cewar Sauran kofunan da Real Madrid ta ɗauka tamkar kofin shayi suke, ma'ana ta ɗauke su ne ba tare da ta fuskaci wani ƙalubale ba bisa la'akari da sukeyi na kofuna guda 7 daga cikin 13 ta ɗaukesu ne a hannun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da basu shahara a duniya ba a halin yanzu, sannan kuma ƙungiyoyi takwas ɗin ƙungiya 1 ce ta taɓa lashe gasar wato Benfica data dauki guda 2 a jere 1961 a hannun Barcelona , sai 1962 kuma a hannun Real madrid.
Har ila yau Real madrid 1955 ta dauka a hannun Reims ta Faransa , 1956 a hannun florentina ta Italiya , sannan ta sake ɗauka a hannun Reims a shekarar 1958, a shekarar 1959 ta ɗauka a hannu Eintracht Frankfurt ta kasar Jamus, 1965 ta dauka a hannun Partizan, shekarar 2000 kuma ta ɗauka ne a hannun Valencia, sai 2002 wanda ta ɗauka a hannun Bayern Liverkusen.
Sauran guda 6 kuma sune: 1957 a hannun Acmilan, 1997 a hannun Juventus, 2013/2014 a hannun Atletico Madrid, 2015/2016 a hannun ATLETICO MADRID, 2016/17 a hannun Juventus, 2017/18 a hannun Liverpool.
TO YAYA ABUN YAKE?
Gabaki ɗaya kofuna 13 da Real Madrid ta lashe kofunane da suke halastattu kamar kowane, kuma ta fuskaci ƙalubale matuƙa kafin ta lashe kowane, babu wanda ta ɗauka cikin ruwan sanyi.
-A bu na farko, daga cikin ƙungiyoyi 6 da Real Madrid ta doke da akema kallon ƙana saida suka baiwa manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa kunya suka fitar dasu kafin su haɗu da Real Madrid a wasan ƙarshe, duk ƙungiyar da suka hadu da ita sai sun basu matsala a shekarar, amma Real madrid ta ɗinga bi taƙansu.
-Kafin Real Madrid ta doke Reims a final a 1955 saida ta doke Acmilan tana kan ganiyarta, daga bisani Acmilan ɗin ta lashe kofin sau 6 a halin yanzu.
-Har ila yau kafin Real madrid ta doke florentina a shekarar 1956 saida ta doke Manchester United itama daga bisani ta lashe kofin sau 3 a halin yanzu.
-Kafin Real madrid ta sake doke Reims a 1958 saida ta doke At madrid wanda ta sami nasarar zuwa wasan ƙarshe sau 3 ba tare data lashe ko guda ba, kuma yanzu haka take matsayin ƙungiya ta 3 mafi girma ta tarihi a ƙasar spain, sannan ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na 10 duniya.
-Kafin Real madrid ta lashe kofin a hannun Frankfurt a shekarar 1959 saida ta doke Barcelona wacce ta lashe kofin sau 5 a halin yanzu, kuma itace ta biyu a cikin manyan ƙungiyoyin ƙasar spain da sukafi girma da tarihi.
-Kafin Real madrid ta ɗauki kofin a hannun Partizan a shekarar 1965 saida ta doke Inter milan, wanda daga baya Inter milan ta lashe kofin sau 4 a halin yanzu.
-Kafin Real madrid ta ɗauki kofin a hannun Valencia a 2000 saida tayi waje da Manchester United a Zagaye na kusa dana ƙarshe (Quater final) daga nan ta sake yin waje da Bayern Munich a wasan dab dana ƙarshe (Sami final). Yanzu haka Bayern munich ta lashe kofin sau 6 kuma tana cikin manyan ƙungiyoyin duniya.
-Sai Uwa uba 2002, kafin Real madrid ta lashe kofin saida tayi waje da Bayern Munich, sannan aka haɗata da Barcelona duk tayi waje dasu ta lashe kafin. Wannan shine sharhin kofuna 7 da ake ganin Real madrid ta ɗauke su ne a sadaka, nasan yanzu mai karatu zaiyi alƙalanci ya raba gardama da kansa.
Sauran Kofuna 6 data ɗauka, ta dauke su ne a hannun Acmilan, Juventus, At madrid, At madrid, Juventus, liverpool.
-Kafin ta ɗauka a hannun liverpool saida ta kori PSG, Bayern Munich, Juventus a 2018.
-Kafin ta ɗauki kofin a hannun Juventus a 2017 saida ta kori Napoli, Bayern Munich, At madrid.
-Kafin ta doke At madrid a final 2016 saida ta doke Roma, Worsburg, Manchester City.
-2014 kafin ta doke At madrid saida tayi waje da zakarun ƙasar jamus gaba ɗaya wato Shelk O4, Dortmund, Bayern Munich.
-Daga cikin Ƙungiyoyin 13 da Real Madrid ta doke guda 4 lokacin suka fara zuwa final kuma tun da Real Madrid ta dokesu basu sake zuwa final ba.
NAKU A KODA YAUSHE WATO
Admin:
Lawan M Ahmad Karaye
07069343044.
0 Comments