A Ranar 7 ga watan June a shekarar 2019, ne Real madrid ta kammala cinikin eden hazard daga Chelsea akan kuɗi €146.1 a matsayin ɗan wasa mafi tsada a ƙungiyar domin ya zamanto makwafin Cristiano Ronaldo daya bar ƙungiyar a shekarar 2018, wanda tun bayan tashin ɗan wasan ƙungiyar take ta nazari da lalube, da hasashen ɗan wasan da suke ganin ya dace ya kwatanta abinda Ronaldo yayi, a cikin wannan yanayi ne suka ɗauko Hazard. Yanzu haka Hazard ya ƙulla Yarjejeniyar zaman shekaru 5 a Real madrid inda zai rinƙa ɗaukar albashin fam dubu ɗari huɗu £400,000 a kowanne mako, a matsayin ɗan wasa mafi albashi a ƙungiyar kuma na 2 a ƙasar spain.
Shin wanne ƙalubalene a gaban Hazard?
1. Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Real madrid da Manchester United sunfi bawa Lamba 7 muhimmanci a filin wasa, yanzu babu wani ɗan wasan da Ragamar ƙungiyar ta ta'allaƙa a hannunsa kamar Hazard, har ila yau Babu ɗan wasan da ƙungiyar ke kallo kamarsa duba da muƙudan kuɗaɗen data kashe wajen ɗauko sa, bugu-da-ƙari, kawo yanzu shine ɗan wasan da magoya magoya bayan ƙungiyar ƙwallon kafa ta Real madrid suke jiran dawowarsa kuma zasu sanyama idanu domin suga rawar da zai taka. Wannan babban ƙalubale ne a gabansa.
2. Ronaldo yazo Real madrid a shekarar 2009 yana ɗan shekara 24 sannan ya kwashe shekaru 9 a ƙungiyar, acikin waɗannan shekaru ya buga wasanni 438, sannan ya jefa kwallaye 451. Saidai Hazard bazai kwashe yawan waɗannan shekaru ba a Real madrid duba da yanzu yana da shekaru 28, Shin kuna ganin Hazard zai iya cin rabin ƙwallayen da Ronaldo yaci?
3. A kowacce kakar wasanni Ronaldo baya Gaza jefa kwallaye 45 zuwa 60 a raga, duba da salon wasan Hazard da Ronaldo ba ɗaya bane, shin kuna ganin zai iya jefa kwallaye 35 a kowacce kakar wasanni?
4. Real madrid suna kashe maƙudan kuɗaɗe su sayi yan wasa domin su lashe Champions League da kuma laliga, akwai bukatar Hazard ya lashe waɗannan kofunan a Real madrid.
5. A wasannin Elcasico da kowanne wasanni da Real madrid ke bugawa Ronaldo shine ja gaba wajen jefa mata kwallaye a matsayinsa na ɗan wasan gefe. Duba da yanzu Real madrid bata da tayayyun ƴan wasa masu jefa kwallaye, shin kuna ganin Hazard zai riƙe wannan kambun?
6. Cristiano Ronaldo ya lashe Kyautar Gwarzon dan wasan duniya wato Ballon D'or guda 4 a real madrid, sannan sai Gwarzon ɗan wasan nahiyar Turai guda 3, sannan sai kyautar Gwarzon dan wasan Fifa. a ƙwallon kafa ana kallon duk ɗan wasan dabai lashe waɗannan kyaututtuka ba ko ɗaya daga cikin su to Tarihinsa bai gama cika ba koda ya lashe kowane kofi a duniya. Daga shekarar 1993 zuwa yanzu mafi akasarin ƴan wasan dake lashe waɗannan kyaututtuka amfi samunsu a Real madrid da Barcelona, a iya cewa wannan kamar wata dama ce da Hazard ya samu, shin kuna ganin zai iya yin amfani da ita?
7. Ronaldo ya lashe kofuna guda 15 a Real madrid, A cikinsu akwai Champions League guda 4. Abisa al'ada ta ƙwallon kafa duk ɗan wasan da yake kwaɗayin lashe champions league to zakaji yana kwaɗayin zuwa Real madrid, gashi hazard bai taɓa lashe wannan kofin ba, wannan shine ya janyo hankalinsa zuwa Real madrid. Shin kuna ganin zai iya bada gudummawa wajen cimma muradin sa?
8. Ronaldo ya kafa manyan Tarihi na cin ƙwallaye guda 26 a Real madrid, acikin su akwai Ɗan wasan da yafi jefama Real madrid kwallaye laliga, champion, dan wasan da yafi jema Real madrid ƙwallaye a matsayin baƙon ɗan wasa a laliga da kuma champion. Shin kuna ganin akwai wani Tarihin Ronaldo da Hazard zai iya karyawa?
9. Hazard ɗan wasane da yake fama da yawan tafiya doguwar jinya tun bayan dawowarsa Real madrid, wanda mafi akasarin ƴan wasa sunfi saurin mutuwa a sanadin Injury, shin Kuna ganin hakan bazai haifar masa da matsala ba?
10. Tunda Ronaldo yazo Real madrid harya tashi babu shekarar da bai shiga sahun yan wasa uku na duniya ba, sannan har ya bar Real madrid yana shiga jerin ƴan wasa 11 na Fifa. A matsayinsa na magajin Ronaldo a Real madrid, shin kuna ganin zai cigaba da riƙe wannan kambun?
0 Comments