Wannan hoto da muke gani hoton wata Makarantar firamare a garin "Isore" Na karamar Hukumar shira Dake Jahar Bauchi wanda ya kasance a yanxu haka ko ingantacciyar Firamare Bare akai ga gina masu Junior da kuma sakandire.
Haƙiƙa ilimi abune mai matukar muhimmanci a rayuwar al'umma, wanda shine haske da yake haska rayuwar kowanne mutum. Idan ka hana al'umma ilimi to babu shakka kamar ka datse masu rayuwa ne. Mutum mai Ilmi ya sha banban da jahili ta kowacce fuska, saboda mai ilmi yana aiki ne ko barin aiki a sakamakon umarnin da ilmin sa zai ba shi, wato a takaice dai ilmin zai kasance tamkar shi ne linzamin da ke jan ragamar hankalin sa da al’amuran sa.
Immanuel Kant masanin ilimin falsafa dan kasar Jamus wanda ba musulmi ba, ya rayu a karni na goma sha takwas yana da imanin cewa: “Batun ilimi da tarbiyya al’amura ne biyu masu girman muhimmanci a rayuwa, kuma sune mafiya matsala da suke addabar mutum a fagen rayuwa”. Har ila yau Kant yana da akidar cewa: “Daga cikin kirkirar mutum akwai samar da daula da tsarin gudanarwa da kuma tsarin neman ilimi da tarbiyya.
Da wannan taƙaitaccen Bayani ne Nake roƙon mahukunta dake wannan yanki da su duba halinda wannan Gari na isore yake ciki na rashin koda tsayyayiyar firamare a wannan gari.


0 Comments