sau dayawa mutane kan yi kukan wayarsu ba ya rike chaji sosai kamar ada,
ya dawo dazaran sun chika shi da chaji se ba wuya ya kare.
daga nan kuwa mafi yawaichin masu amfani da waya su suke saurin lalata wayansu ko batirin wayansu.
dan hka a yanzu zan jero wasu kuskurori da aka fi yi wanda ke jawo saurin lalachewar waya ko batirin wayar.
daga chiki akwai:
1- BARIN WAYA HAR SE YA KARE KAFIN A SA A CHAJI.
yin hakan kuskure ne sosai, bayyanan illarsa ba a lokachi guda bane, da kadan da kadan ne ke yin illa wa batir, a hankali a hankali wataran se mutum ya ga jimawan rike chaji a batir dinsa ya ragu, se ya zama ba ya jimawa da chaji ya kare.
dan haka kadaina barin chaji har seya kare kafin asa shi a chaja shi yanadakew dazaran ya kai 20% ko 15% a je a chaja.
in kuma me nuna yanka yanka ne dazaran ya je saura yanka 1 a gaggauta sanya shi a chaji.
Domin ko kai kanka ma idan ka fara jin yunwa ai kakan nemi abinci ka chi ne tun kafin tsananin yunwa ya nemi kashe ka, kakan yi chajin kanka.
Sannan kuma mutumin da yake yawan zama da yinwa ai Qualitinsu ba ya yin daya da wanda be cika zama da yunwa ba To ita na'urar waya ma hka ne.
2- BARIN RIGAR WAYA A JIKIN WAYAR YAYIN YIN CHAJI.
shi waya yana fitar da zafi a lokachinda ake yin chaji, dan hka in ana so waya ta kasanche ba ta kaiwan tempreature na zafin da zai yi saurin mata illa to sai a rika chire ta daga rigarta in za a yi chaji domin wannan zafi ya samu fita chikin sauki ba tare da ya taru a jikin waya sosai ba. domin yin chaji a yanayin nau'in tempreature na zafi kan iya lalata inganchin batir, ko ma ya lalata batir gabadaya.
3- CHAJIN WAYA A INDA BE DACHE BA.
yana da kew a kula da yanayin gurin da za a sa waya yin chaji, domin su wayoyi suna da tsari na adadin nau'in yanayin dake musu illa da kuma adadin da ba ya musu.
dan hka yin chajin waya a guri me zafi zai iya kara yawan adadin zafi ma wayan, idan adadin ya haura yanda yake daidai da wayan se ya zama ya fara illata waya.
to hka ma in a gun sanyin da ya wuche adadin yanda aka tsara ma waya lokachin qirarta.
.
4- SANYA WAYA A CHAJI YAYIN KWANCHIYA BARCHI YA KWANA YANA CHAJI.
a takaiche barchin dare akan kai awoyi 5 ko 8 ana yi kafin a tashi, kai kuma wayarka a tsarinsa in an sa chaji yakan chika a chikin awa 2 ko 3, a hkan kuma ka sanya masa chaji lokachin barchinka har ya gama chikansa baka chire ba, wannan dalili kansa batir yayi ta wahaluwa, a kwana a tashi in kana hka ba wataran se ya zama ka yi saurin fiskantar matsalar batirin wayarka. sakamakon wannan ova chaji dakake masa,
ya zama ba ya rike maka chaji sosai kamar ada.
dan hka abinda ya fi kew shine ka yi chajin wayarka kafin ka kwanta barchi.
.
5- DANNA MA WAYA KOWANE IRIN CHARGER:
yana dakew ka san adadin lokutan da wayarka ke chika da ainehin chajar wayarka wanda tazo da shi tun farko.
daga nan ka kaurache wa nau'in chajar dakasan yake chika ta kafin wannan lokutan da aka kayyado ta akai
6- BARIN WAYA A CHAJI HAR SE LALLAI YA KAI 100 PARCENT.
yin hkan kuskure ne, domin indai ba akan idonka zai cika hundred din, kuma dazaran ya cikan ka cire ba akwai matsala, kow da kuwa be wuce minti daya da cikanba.
Dan hka indai ka sa chaji dazaran ka ga ya kai daf da cika to ka raba shi daga chajin.
7- QIN YIN CHAJI MA WAYAR DA AKA AJIYE BA A AMFANI DA ITA.
akwai waenda in suna da wayar da ba su bukatar amfani da ita sukan ajiye ta na tsawon kwanaki ko watanni ko ma fiye da hka ba tare da suna dauka su chaja ta ba.
Yin hkan kuskure ne.
Dan hka idan ka san za ka yi irin wannan aji ma waya to ka tabbatar ka chaja shi tukun.
Yana dakew ka ajiye shi da adadin yawan cajin da ya kai 50 percent ko fiye da hka.
Sannan kuma duk bayan wasu 'yan kwanaki ka rika dauka kana sawa a chaji, kar ya zama ba ka mata chaji kwata kwata.
Yin hkan na iya lalata maka batirin waya.
.
8- YAWAN CHAJA WAYA TA HANYAR AMFANI DA WIRELESS CHARGER.
yawan yin chaji da wannam na iya saurin lalata maka batir ko ma wayar, Sakamakon dumin da kan dauka daga jikin wannan "wireless charger" din.
Shi amfanin irin wannan sai in a lokachin tsananin sanyi kokuma idan asalin gurin yin chaji ya samu matsala.
Don qudun kar waya ta zama ba cahaji a lokacin sai ayi amfani da irin wannan chaja kafin a gyaro asalìn gun chajin.


0 Comments