Wani bincike daga Cambridge university london







Za mu yi ta nuna musu ayoyin mu acikin sammai da kassai, da kuma kawunan su, har sai ya bayyana musu a fili cewa shi Al-qur'ani gaskiya ne daga wurin Allah ne".
Suratul Fussilaat ayata 53.
Wani bincike ne naga Cambridge University dake London suka yi, tare da hadin gwuiwar manyan masana ilimin cikin kasa da abinda ke kan kasa, wato (Geologists) na duniya, cewa bincike ya tabbatar da cewa wannan duniyar da muke cikin ta, idan kaje tsakiyar duniya wato "Center of the World", a karkashin kasa, can 'kasa sosai, suka ce an halicci wurin ne da 'karfe.
.
Karfe mai yawa mai fadin gaske, suka ce "Actually the center of the Earth is made up of Iron, billions years ago".
Wannan binciken da suka yi shekaru 35 da suka wuce, an sake mai maita shi a "Stanford University, California" United States of America, wanda wata Professor mai suna Wendy Maop ta jagoranci binciken a 2013, kuma gidan Radion BBC, wato sashen Turancin su (English) ya rubuta wannan binciken, wanda wani Editan su mai suna "Chris Baraniuk" ya rubuta ranar
13 August 2015, sun yi binciken ne ba tare da Al-qur'ani ba, domin basu ma yarda da Al-qur'anin ba, yanzu haka ina da rubutun a ajiye.
.
Amma abinda zai baka mamaki shine Al-qur'ani babu littafi kamar sa, bari na kawo maka wasu abubuwa kadan, zaka kara yarda da cewa Al-qur'ani littafin Allah ne da aka kawo mana daga sama.
:
Tsakiyar duniya an yi shine da 'karfe:
Al-qur'ani yana da Surori 114.
Kayi lissafi ko ka dauki wayar ka kayi lissafi, ka raba 114 gida biyu
114÷2 = 57.
Zai baka 57, 57 shine tsakiya, babu ragi babu kari.
Sai ka dauki Al-qur'ani ka, kaje ka bude Surah ta 57 zaka sunan surar shine (Suratul Hadid) wato (The Iron)....
Allahu Akbar....
.
Sannan idan ka koma ilimin Chemistry, a periodic table na Elements, zaka ga cewa Iron yana da Atomin Number 26 ne....
Kaje ka bude Suratul Hadid 'din, ka fara 'kirga ayoyin har da Bismillah....
Abin nufi kace (Bismillahir Rahmanirrahim) aya ta 'daya.
Idan kaje kan Aya ta 26 zaka ga itace exactly ayar da tayi magana akan karfe (Iron).
Saboda koda a Chemistry Atomic number na Iron is 26.
Sannan idan ka fara 'kirga sunan "Allah" daga ayata farko, idan kazo dai ayata 25 zaka ga a wurin ne yawan sunan Allah ya cika na 26, idan kuma ka kirga harda Bismillah to idan kazo ayata 26 wurin ne sunan Allah ya cika na 26, kamar yadda kaga Iron yake da Atomic number 26 a chemistry.
Sannan Suratul Hadid itace Surah ta 57, a Chemistry kuma number 57 is one of the isotopes of Iron.
.
Acikin binciken zaka ga inda suka ce sun tabbatar cewa 'karfe ba daga cikin kasa yake ba asali, daga wani wuri aka kawo shi, shekaru biliyan hudu da rabi da suka wuce a lissafin su.
Already dama Al-qur'ani ya tabbatar da cewa 'karfe an sauko dashi ne daga sama Allah yace:
ﻭﺍﻧﺰﻟﻨﺎ ﺍﻟﺤﺪﻳﺪ
"Kuma mun saukar da karfe (daga sama)", wato zuwa 'kasa.
Sune suka gano yau, amma tun sama da shekaru dubu 1,400 manzon Allah yazo da wannan information din.
.
Zan tsaya a nan, amma wannan somin tabi ne, akwai wasu bincike da na riga na same su guda 41 na rubuta su, na ajiye su, zan rinka rubuta su da Hausa a nan Facebook, a hankali a hankali wanda zai sa ka gane Al-qur'ani babu kamar sa na rantse da Allah.
Wallahi akwai binciken da idan nazo na rubuta shi anan zaka rike baki kace Subhanallah, wannan duk acikin Al-qur'ani?

Post a Comment

0 Comments