Tarihin ƙwallon ƙafa na nahiyar Afrika ba za'a taba mantawa da RASHIDI yekini ba





Rashidi Yekini Tsohon ɗan wasan gaban Super Eagles Najeriya, shine yazo na uku a cikin jerin ƴan wasa 10 na Najeriya da babu kamar su a tarihi.
Rashidi Yekini an haife shi a ranar 23 ga watan October a shekarar alif 1963 a garin Kaduna dake arewacin Najeriya.
A Tarihin ƙwallon ƙafa na Najeriya ba'a taɓa samun ɗan wasan daya kware wajen jefa kwallo a raga kamar Rashidi Yekini ba, kuma shine ɗan wasan da yafi jefama Najeriya kwallaye a wasanni.

Ya fara ƙwallon ƙafa a shekarar alif 1981 a ƙungiyar UNTL Kaduna. A shekarar 1982–1984 yayi wasa a ƙungiyar  Shooting Stars Dake buga gasar ajin ƙwararru na cikin kofin Najeriya Inda ya buga wasanni
53 ya jefa kwallaye 45.

Rashidi Yekini ya ƙare ƙwallonsa ne a nahiyar Afrika, kuma yana cikin jerin ƴan wasan cikin gida na nahiyar Afrika da babu kamar su. A Tarihinsa ya buga wasanni 311, sannan ya jefa kwallaye 201.

Ɗan wasan ya rasu a garin Ibadan dake jihar Oyo a ranar 4 ga watan May a shekarar 2012 yana ɗan shekara 48. Sai dai har yanzu Tarihin wannan qwallon yana cikin zuciyar ‘yan Nigeria, musamman waɗanda suka kalli wasan a lokacin saboda  muhimmancinsa da kuma kalar murnar da Yakini yake alokacin daya zura ƙwallon.

Yakini, wanda ya ke cikin tawagar Super Eagles wadda ta mamaye nahiyar Africa a shekarun 1994 har yanzu shine xan wasan da yafi kowanne dan wasan Nigeriya zura qwallo a raga inda ya zura qwallaye 37 a tarihinsa.
A ranar 21 ga watan Yunin shekarar 1994 Marigayi Rahidi Yakini ya kafa tarihi a gasar cin kofin duniya inda ya kasance dan wasan Nigeriya na farko daya fara zura qwallo agasar cin kofin duniya a wasan Nigeriya na farko da qasar Bulgeria a birnin Dallas na ƙasar Amurka

Sai dai har yanzu tarihin wannan kwallon yana cikin zuciyar ‘yan Nigeriya, musamman wadanda suka kalli wasan a lokacin saboda muhimmancinsa da kuma kalar murnar da Yakini yayi alokacin daya zura ƙwallon.
Bayan da Rashidi ya zura qwallon a raga ne ya shiga cikin ragar ya riqe zaren rgar yana murna sannan yana zubar da hawayen murna a lokaci guda kuma yana furta sunansa inda ya ke cewa “Rashidi Yakini”Tsohon dan wasan Super Eagles, Matiu Adepoju, ya bayyana Yakini a matsayin dan wasan da qasar nan ba zata taba mantawa dashi ba saboda ƙwallayen daya zura a raga sannan kuma idan ana maganar kofin duniya dole a saka sunansa acikin labarin Nigeria.

Rashidi Yakini shine dan wasan gaba na Nigeriya wanda har yanzu ba’ayi kamarsa ba sannan ya lashe kyautar Gwarzon dan qwallon Africa a shekarar 1993 kuma a lokacin da yake kan ganiyarsa yana bawa kowanne mai tsaron raga tsoro musamman idan ya mallaki qwallon a raga a bakin raga.
Duk wanda ya san Rashidi Yakini ya san yadda ya ke da qarfin buga qwallo a raga
kuma a haka ne aka bashi sunan “Sarkin Zura Qwallo A Raga’ kuma har yayi ritaya
babu wani xan wasa da aka bashi suna irin na Rashidi Yakini.

Shekaran jiya Litinin ne ɗan wasan ya cika shekara 8 da rasuwa. Muna addu'ar Allah ya jiƙansa.


Post a Comment

0 Comments