Jaridar Vanguard sun tabbatar da jita jitar da ake yadawa akan batun Nada Farfesa Gambari matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.
Farfesa Ibrahim Gambari, dan asalin jihar Kwara ne, yana daga cikin mutanan kirki da ake ganin girmansu a Najeriya da Nahiyar Afurka da kuma majalisar dink in duniya.
Kasancewarsa ba wani sanannen dan wata jam'iyya ba a Najeriya, wannan zai bashi kwarin guiwa wajen yin adalci ga kowane bangare na 'yan siyasar kasarnan.
A matsayinsa na kwararren Jami'in diplomasiyya, wanda tarayyar Afurka da majalisar dinkin duniya suka sha yaba masa, muna ganin wannan zai taimake shi wajen nemowa Gwamnatin Buhari dama Najeriya mutunci a idon duniya.
Gambari ya taba zama Ministan harkokin wajen Najeriya a zamanin Gwamnatin Buhari ta mulkin Soja. Bayan mukaman da ya rike irin su Manzon musamman na tarayyar Afurka da majalisar dinkin duniya a yankin Darfur da Angola da gurare da dama.
Shaidu sun tabbatar da kwarewarsa wajen tafiyar da al'amura masu sarkakiyar gaske, da kuma warware dambarwa da kitumurmura Kala kala a nahiyar Afurka.
Muna masa fatan alheri, Allah ya bashi Ikon yin aiki da gaskiya da kuma tsoron Allah.


0 Comments