Iyayen Mario Balotelli yan Asalin ƙasar Ghana ne dake yankin nahiyar Afrika, wanda gudun Hijira ya kaisu ƙasar Italiya inda suka fara sauka a wani gari mai suna Bagnolo Mella dake yankin Brescia a ƙasar ta Italiya. A shekarar 1993 lokacin Mario Balotelli yana ɗan shekara 3 ya tsinci kansa a wurin kula da marasa galihu wanda suke rayuwa shida iyayensa a sakamakon iyayensa ba zasu iya ɗawainiya dashi ba da kula da lafiyarsa.
A wancan lokaci ne ya faɗa hannun wani hamshakin attajiri wato Jewish da matarsa Silvia, kasancewar basu taɓa haihuwa ba tasa ya ɗauke sa zuwa gidansa inda yake kawo sa wajen iyayensa a kowanne mako. Ya taso cikin kulawa, jindadi da kuma ƙasaita.
A ranar 13 August shekarar 2008 ne ya cika shekara 18, inda a daidai wannan lokaci ne ya sami shaidar zama ɗan ƙasar Italiya.
Mario Balotelli ɗan wasan gaba ne mai hazaƙa daya kware wajen jefa kwallo a raga. Mario Balotelli ya taso cikin tsangwama da fuskantar ƙalau bale na wariyar launin fata, Hakane yasa ɗan wasan yake da yawan fushi, sannan yayi ƙaurin suna a wajen rashin ɗa'a sannan baya ɗaukar raini a ko ina Yake.
Balotelli ana masa lakabi da "Super Mario". Kafofin watsa labarai sun bayyana Balotelli da sananne saboda kasancewarsa mai wahalar sha'ani, amma duk da haka yakan sauraron manema labarai domin amsa tambayoyin da ake yi masa wanda galibin su abin dariya ne.
Wani lokaci José Mourinho ya bayyana shi a matsayin mutum "wanda ba zai iya taɓa sarrafuwa ba".
Mario Balotelli Sam baya girmama masu horarwa, domin sunsha yin rikici da joses mourinho a lokacin yana Inter Milan. Mourinho ya bayyana cewa," zan iya rubuta littafi mai shafi 200 akan rayuwarmu da Baletolli a Inter, amma saidai labarin zai kasance kamar wani wasan kwaikwayo mai cike da ban dariya" Mourinho ya ƙara da cewa "Wata rana a kakar wasanni ta 2009/2010 zamu buga wasa da Kungiyar Kazan a gasar cin kofin nahiyar zakarun Turai, a lokacin dukkan yan wasan mu na gaba suna jinya sai iya Mario Balotelli ya rage mana, gaskiya A lokacin muna cikin matsala. Minti 42 da fara wasa ne Balotelli ya sami katin gargaɗi. Da aka tafi hutun rabin lokaci shi kaɗai ne ɗan wasan dana saurara saida na kwashe minti 14 ina lallaɓasa tare da masa gargaɗin cewa, bazan chanja ka ba sabida kai kaɗai ne ka rage mana, don haka ka nutsu kada ka doki kowa, kada ka zagi kowa, kayi wasa kawai. Idan alƙalin wasa yayi kuskure kada kayi magana, har ila yau idan wasu na yima alkalin wasa magana akan kuskure kada kaje wajen, ɗan wasan ya nuna ya gamsu. Amma minti ɗaya da dawowa daga hutun rabin lokaci ɗan wasan yayi ƙeta aka basa jan kati.
A watan Yuni na shekarar 2010, Balotelli da abokansa sun harba bindiga sama a cikin taron jama'a a wani wurin shakatawa da ake kira "Piazza della Repubblica a birnin Milan.
Ana yawan tafka muhawara akan ɗan wasan shin Mahaukaci ne ko mai hankali? Kodayake mutane da dama sun kirasa da "mahaukaci" kamar yadda mai horarwarsa Roberto Mancini ya bayyana. sau da yawa, Balotelli ya yarda cewa "Shi daban ne da kowa, sabida wani lokacin yakan aikata baƙon abu da ba'a taɓa ji ko gani ba".
Kuma A shekarar 2010 ɗin ne aka dauki hoton shi tare da wasu mutane biyu
Waɗanda an tabbatar da cewa yan Mafia ne.
Komawarsa Manchester City keda wuya ne ɗan wasan ya shiga ƙungiyar matsafa, inda yake bayyana alamomin ƙungiyar. Magoya bayan Manchester City suna yawan rera masa waƙa a kai a kai, tare da waƙoƙin da ke nuna ayyukansa. Sannan Mawaƙi Tinchy Stryder ya rubuta masa waƙa a cikin girmamawa ga Balotelli, ".
Bayan ya koma ƙungiyar ƙwallon kafa ta Mancity ne yasa aka buga masa riga dauke da kalmomin "Why Always Me? " ma'ana (Me yasa koyaushe ni?) itace rigar da Balotelli ya saka a matsayin ƴar ciki, inda ya bayyana ta a watan Oktoba 2011 bayan ya jefa kwallo a ragar Manchester United.
A cikin Disamba 2011, Balotelli ya karya dokar hana fita na awanni 48 kafin wasan Manchester City da Chelsea don zuwa gidan da ake hada-hada. An yanke masa hukuncin tara a sakamakon an tabbatar da yana cikin hayyacinsa kuma ko kaɗan baya shan barasa.
Kawo yanzu a Tarihin ƙwallon ƙafa ba'a taɓa yin ɗan wasa mara ɗa'a kamarsa ba, musamman a fagen wasanni da mu'amala ta yau da kullum. Mario Balotelli yana da tarin laifuka.
Ya buga wasa a ƙungiyoyin ƙwallon kafa guda 8.
2006–2007 a ƙungiyar Lumezzane ya buga wasanni 2 bai jefa ko kwallo 1 ba.
2007–2010 ya buga wasa a Inter Milan, ya buga wasanni 59 ya jefa kwallaye 20.
2010–2013 ya buga wasanni a Manchester City 54 sannan ya jefa kwallaye 20.
2013–2014 ya buga wasanni a Milan, ya buga wasanni 43 ya jefa kwallaye 26.
2014–2016 Liverpool, ya buga wasanni 16 ya jefa kwallo 1.
2015–2016 → Milan (loan) ya buga wasanni 20 ya jefa kwallo 1.
2016–2019 Nice, ya buga wasanni 61 ya jefa kwallaye 33.
2019 Marseille , ya buga wasanni 15 ya jefa kwallaye 8.
2019–zuwa yanzu Brescia ya buga wasanni 19 ya jefa kwallaye 5.
A ƙasar Italy daga 2008 zuwa yau ya buga wasanni 52 sannan ya jefa kwallaye 20.


0 Comments