Kamar yadda aka sani, duk wanda ya sha ko yaci abinci da mantuwa a lokacin da yake azumi yana da azumin, azumin sa bai karye ba, saboda manzon Allah ya fada a Hadisin Imamu Ibnu Khuzaimah yace "Wanda yaci ko yasha da rana a watan Ramadhana babu ramuwa akan sa kuma babu kaffara".
.
Amma hukunci wanda ya sadu da mace da ranar watan Ramadhan, hukuncin guda uku ne:
1. Na 'daya zai yi ramuwa, abin nufi zai biya wannan guda dayan da ya karya ta hanyar saduwa da mace.
2. Na biyu, zai yi Kaffara, kaffaran kuma shine zai yi azumi sittin a jere (ko azumin watanni biyu a jere) ba tare da ya sha ruwa ba.
3. Na uku zai yi istighfari tare da tuba, da yawaita aiyukan alkhairi saboda ya aikata laifi mai muni.
.
Hukuncin duk 'daya ne da wanda ya sadu da matar sa da kuma wanda yayi zina.
Sai dai shi wanda yayi zina laifuka biyu ne akan sa, laifin karya azumi da laifin Zina, wanda yake da aure kuma laifin karya azumi ne kawai akan sa.
Amma dai duk hukuncin daya a wurin Kaffara da ramuwa, zasu biya daya, sannan suyi azumin watanni biyu a jere.
.
Sai mutum na uku, wanda ya sha ruwa da gan-gan (intentionally) ba tare da rashin lafiya ba, ba tare da wani kunci mai tsanani ba, abin nufi haka kawai sai yasha ruwa da rana ko yaci abinci, Malamai sunyi maganganu uku game da hukuncin irin wannan mutumin:
:
1. Wasu Malaman suka ce zai biya 'dayan da ya sha, sannan zai yi kaffaran azumi sittin, sun ce hukuncin sa daya da wanda ya sadu da mace.
2. Malamai bangare na biyu suka ce zai biya azumi dayan da ya sha, sannan zai yi kaffaran azumi daya, wato zai yi azumi biyu kenan.
3. Na uku suka ce zai biya azumi dayan da ya sha ne kawai, babu kaffaran azumi sittin akan sa domin bai sadu da mace ba, sannan babu nassin da yace yayi azumi daya bayan yayi ramuwan dayan.
.
Magana ta uku, ta karshen itace dai dai in sha Allah.
Sai mutum na hudu, ita kuma macen da aka sadu da ita menene hukuncin ta? itama sittin zata yi ko kuma?
In sha Allah a rubutu na gaba zamu amsa wadannan tambayoyin.
.
Sannan ina bayar da hakuri ma wadanda suka saba bibiyar rubuta na ban sanya reference (Masaadir) ko Source acikin rubutun ba, saboda rashin karfi da nake fama dashi, amma wadannan bayanan suna cikin dukkan littattafan da aka sani wadanda suke sharhin hukunce-hukunce.
Allah yasa mu dace....


0 Comments