Salama alaikoom da fatan an wayi gaari lafiya
Akwai wasu abubuwa guda biyu, wanda na gan su a wasu Hadisai na manzon Allah (S.A.W) suna da tsananin hatsari ga masu aikata su, amma da yawa daga cikin mutane basu 'dauke su da muhimmanci ba, wadannan abubuwan guda biyu za suyi tasiri matuka akan masu mulki da talakawa a wannan lokacin na coronavirus, manzon Allah yaja kunne yayi gargadi game da lamarin, saboda hatsarin su
.
Abu na farko yin 'karyar abinda babu shi:
Duk lokacin da kayi karyar abinda baka dashi sai Allah ya jarrabe ka da rashin abin, idan kuwa ciwo ne kayi karyar sa sai Ubangiji ya jefa maka ciwon da sai kayi nadamar yin wannan karyar.
Shugabannin mu a jihohi da kasa gaba daya suna bayyana cewa akwai cutar corona-Virus fiye da yadda take a zahirin gaskiya, wurin da babu cutar sai ace akwai, adadin da ba'a kai ba sai suce an kai.
.
Abinda nake jiye mana tsoro shine idan Allah ya juya wannan lamarin kowa zai ji a jikin sa, kuma masu hankali ne kawai zasu gane cewa karyar da aka yi akan cutar zai iya halakar da dubban mutane.
Dan haka karya da bayyana adadin da babu su bai kamata shugabannin mu suyi mana haka ba, saboda kaucewa fushin Ubangiji.
.
Abu na biyu da manzon Allah yayi gargadi akai shine (Izgili) ko ba'a ko habaici akan wani abinda yake a zahiri.
Duk abinda kasan cewa ba'a yin wasa da lamarin sa a zahiri toh kada kayi wasa dashi, kada kayi ba'a ko habaici ma wannan lamarin.
Misali:
Masana harkar kiwon lafiya sun yi ta kira zuwa ga mutane dasu rika wanke hannun su, saboda gudun kamuwa da cutar corona-Virus, sannan su zauna a gida a lokacin da ba'a ce su fito ba, har mutane suke 'karawa da cewa (in anji yunwa a sake wanke hannu) duk saboda izgili da habaici, baka tunanin Allah zai iya hukunta ka da wannan izgilin?
.
Abinda zai baka mamaki yadda mutane suka mayar da wannan maganar abin yiwa izgili da habaici, cewa a wanke hannu a zauna a gida, ko kuma jama'a kuyi hakuri: a zahiri ba haka abin yake nufi ba amma mai-maita shi da mutane suke yi sai ya mayar dashi ba'a da habaici, wanda zai iya sabbaba maka fitina.
Manzon Allah yaga wani mutum yana cin abinci da hannun hagu sai yace bawan Allah ka daina ci da hagu kaci da dama, sai mutumin ya mai-maita maganar da izgili, tun daga ranar har ya mutu hannun sa bai sake iya kai hannun sa bakin sa ba, sai dai a bashi abinci a baki,
hannun sa ya 'kage saboda izgili da yayi da wata magana.
.
Ina yawan gani mutane suna sakawa a WhatsApp ana kwai-kwaiyon muryar shugaban kasa ana cewa toh hakuri? kuyi hakuri muna baku hakuri!!!
Kaga irin wadannan kalaman suna daga cikin kalaman da suke fusatar da Ubangiji, duba da wadancan hadisan, kada Allah ya jarrabe ka da wahalar da dole kayi hakurin da baka taba tsammani a rayuwa ba, dan haka muyi hankali jama'a.
.
Idan kana furta hakan ne da nufin izgili ko habaici hakika ka sabawa manzon Allah, domin idan Allah yayi fushi da kalaman bawa kalaman ne zasu zamo jarabawar sa, sai Ubangiji ya jarrabe ka da rashin lafiyar da zaka kasa hatta wanke hannun.
Allah ya tsare mu, amma mu sani ba'a yin izgili ko wasa ko kakaci a lokacin da wata Musiba take tare da jama'a, ko wahala ta rayuwa.
Saboda Allah zai ga cewa madadin ka koma zuwa ga Allah ana cikin wahala kai ka mayar da abin wasa da izgili kuma, dan haka sai wahala ta sake sauka.


0 Comments