Taƙaitaccen Tarihin Paulo Maldini



TARIHIN  PAULO MALDINI

Nasan wasu daga cikin masu karatu zasu iya cewa wanene kuma paulo maldini?
Paulo maldini dan kasar italiya ne kuma tsohon dan wasan Acmilan.  Cikakken sunansa shine (Paolo Cesare Maldini) , an haifesa a ranar 26 ga watan June a shekarar 1968 a birnin Milan dake kasar italiya .

 A Tarihin kwallon kafa Ana kallon maldini a matsayin dan wasan baya da babu kamarsa a kasar Italia, da Acmilan kai dama duniya baki daya, sannan yana cikin jerin yan wasan da babu kamarsu a duniya.
Maldini ya shahara matuka a wajen buga lamba 2 da lamba 5 ko 6 wato ( left back and central defender).

A bisa Tarihi da bincike Tun tasowar Maldini bai taba yin wasa a kowacce kungiya ba sai Acmilan tun yana yaro kankane, kuma anan ya ajiye kwallonsa. Hakan ne ya basa damar zama dan wasan da yafi kowa buga gasar cin kafin kasar italiya wato (Seria A) inda ya buga wasanni 647, yanzu haka shine dan wasan da yake biye da Iker casillas na wadanda sukafi kowa buga gasar cin kofin nahiyar turai, har ila yau shine dan wasan da yafi bugama Acmilan wasanni kuma inda ya buga mata wasanni 902 kuma yana daga cikin yan wasan da sukafi kowa dogon zamani a kwallon kafa inda ya buga kakar wasanni 26 , sannan ya dauki shekaru masu tsayi yana matsayin kyaftin din Acmilan da kuma kasar italiya, shiyasa ake masa kirari da sarki na kyaftin, wanda ake masa kallon wani jagora a kwallon kafa na wannan karni.

Maldini yana daga cikin yan wasa 18 na duniya da iya sune suka sami nasarar buga wasanni sama da dubu a duniya.
Yanzu haka maldini shine Daraktan wasanni a kungiyar Acmilan, kuma shine mallakin kungiyar Miami FC.

1978–1987

Ya fara kwallon kafa a checkered 1978 a karamar kungiyar kwallon kafa Acmilan har zuwa shekarar 1985 kimanin shekaru 7. Ya taka rawar gani matuka, inda hakan ne ya basa damar buga wasa a babbar kungiyar Acmilan.
 Ya fara bugama babbar kungiyar Acmilan wasa a kakar wasanni ta 1984–85 yana da shekaru 16 a sakamakon raunin da dan wasan baya na Acmilan yaji wato Sergio Battistini, ya taka rawar gani a wasan.  Akarshen kakar wasan ne lokacin daya cika shekaru 17 aka damka masa riga mai lamba 3 , daga nan ya zama cikakken babban dan wasa a Acmilan, kuma ya lashe gasar Coppa Italia a shekarar ta 1985.

NASARORIN DAYA SAMU A KWALLON KAFA.

Lokaci bazai bani damar rubuta Tarihin paulo maldini ba, sabida Tarihinsa idan Rubutawa za'a littafi ne mai zaman kansa , saidai in Dan takaita sa.

Maldini ya Buga wasanni dubu a Tarihin rayuwarsa, amma saidai harda wasannin sada zumunci na kungiya da kuma kasarsa,    inda ya jefa kwallaye 36 a kungiyarsa da kasarsa baki daya.
Maldini ya lashe kofuna guda 25, Champions League 5, Serie A guda 7,Coppa Italia 1, Supercoppa Italiana guda 5, European
Super Cups guda 5, Intercontinental Cups guda 2, club world cup guda 1.

Ya lashe kyautar (UEFA Club Football Awards), Gwarzon dan wasan  baya na italiya (Serie A Defender of the Year Award). Da sauran manyan kyaututtuka . saidai Babban Tasgaro da Da maldini ya samu a kwallon kafa shine, bai lashe world 🌎 cup ba amma sai dai yaje final a shekarar 1994, sannan sai kyautar  fifa Ballon D'or inda  masana kwallon kafa ke  kallon cewar yana daga cikin yan wasan da sukayi bajintar da ta kamata su lashe kyautar amma basu lashe ba. Saidai yazo na biyu a shekarar 1995 da George Weah ya lashe , wato dan Africa tilo daya taba lashe kyautar a Tarihi. Sannan Maldini shine yazo na uku wajen lashe kyautar a shekarar Ballon 1994 da 2003 amma bai lashe ba saidai a shekarar ya shiga cikin ( FIFA World Cup Dream Team) .

Wannan shine kadan daga rawar da Paulo maldini ya taka a kwallon kafa da har abada baza'a manta dashi ba. Wanda daya daga cikin members na wannan gida ya bukaci na kawo wato SULAIMAN MUHAMMAD , ina godiya da wannan Tambaya taka, kuma zan dinga amsa irinta aduk lokacin da aka bukata.


Post a Comment

0 Comments